IQNA

10:45 - February 27, 2013
Lambar Labari: 2503213

Ana Zargin Wasu Kasashe Da Hannu Wajen Haifar Da Ayyukan Ta'addanci A Iraki

Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Turkiyya tana bawa wasu yan adawar kasar Iraqi horar soje karkashin wata kungiya mai suna sojojin yentacciyar kasar Iraqi, wacce zata share fagen kifar da gwamnatin Priminista Noori Al-Maliki. Wata jaridar kasar Turkiya mai suna Aydinlik Gazete ce ta bayyana haka.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, majiyar ta ce wadannan mutanen sun fara samun horo ne tun shekarar da ta gabata a cibiyar horar da jami'an tsaron kasar Turkiya ta Golbasi a yankin Ankara. Yan tawayen dai suna da dangantaka da tsohon mataimakin shugaban kasar ta Iraqi Tariq Al-hashimi wanda yake samun mafaka a kasar ta turkiyya, ton lokacinda ya arce daga kasar kan zargin tallafawa ayyukan ta'addanci, inji jaridar.

Aydinlik Gazete ta kara da cewa tsohon na hannun damar tsohon shugaban kasar Iraqi Sadam Husain, Izzat Ibrahim al-Douri yana aiki tare da gwamnatin kasar Turkiyya don ganin bayan gwamnatin Priminista Noori Al-Maliki. A farkon wannan watan da muke ciki ne tashar television ta Al-Arabia mallakin kasar saudia ta nuna Izzat Ibrahim al-Douri yana kodaitar da masu zanga zangar nuna kiyayya da gwamnatin Noori Al- Maliki na su ci gaba da tada kayan baya har zuwa faduwar gwamnatin kasar ta Iraqi.

Gwamnatin kasar Iraqi ta bada umurnin rufe kan iyakar kasar da kasar Jordan a safiyar yau laraba. Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani jami'in tsaro na kan iyakar yana cewa sun tsaida dukkan ayyukan a kan iyakar da ke Traibil a jihar Ambar. Colonel Mahmoud Mohammed Ali ya kara da cewa sun tsaida shiga da fitar motoci manya mannya da kanana da kuma zirga zirgan mutanen tsakanin kasashen Jordan da kuma Iraqin.

Yankunan Anbar da kuma da kuma ramadi na kasar Iraqi dai suna fama da tashe tashen hankula tu watan Decemban da ta gabata , bayan da gwamnatin kasar ta sa aka kama masu tsaron daya daga cikin ministocinsa dan yankin kan tuhumar ayyukan ta'addanci. Masu zanga zanga a yankunan da mafi yawan mazauna wurin babiyan mazhabar sunna ne sun rufe hanyoyin shiga kasashen Syria da kuma Jordan a kokarin da suke yin a tilastawa gwamnatin Priminista Nuri al-maliki sallamar wadanda aka kama ko kuma kira da ma raba kasar.

1195586
































captcha