IQNA

22:37 - March 16, 2013
Lambar Labari: 2511992

An bukaci kungiyar kasashen musulmi da ta bayyana matsayinta kan keta alfarmar kur'ani a Bahrain

Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin manyan malaman addini kuma limamin birnin Najaf ya bukaci kungiyar kasashen musulmi da ta nuna matsayinta kan cin zarafin da jami'an tsaron kasar Bahrain da na mamamyar Saudiyya da ke kasar suka yi kan kur'ani mai tsarki.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Sayyid Sadruddin Kubanchi daya daga cikin manyan malaman addini kuma limamin birnin Najaf ya bukaci kungiyar kasashen musulmi da ta nuna matsayinta kan cin zarafin da jami'an tsaron kasar Bahrain da na mamamyar Saudiyya da ke kasar suka yi kan kur'ani mai tsarki a cikin kasar da sunan murkushe masu dawa da mulkin kama a karya .

Jami'an tsaron kasar Bahrain sun tarwatsa masu Zanga-zangar da su ke kokarin isa dandalin lu'u-lu'a da ke tsakiyar birnin Manama. Jami'an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma kulake da abubuwa masu kara domin tarwatsa masu zanga-zangar maza da mata da kuma kananan yara. Zanga-zangar ta yau ta zo ne a matsayin share fage na babbar zanga-zangar da 'yan hamayyar siyasar kasar su ka kira domin tunawa da zagayowar lokacin fara neman kawo gyara ta fuskar siyasa a kasar.

A ranakun alhamis da juma'a ne za a yi gagarumar Zanga-zanga da kuma yajin aiki a duk fadin fadin kasar saboda tunawa da cika shekara biyu daidia da fara yunkurawar al'ummar kasar.

1204720

















captcha