IQNA

21:48 - March 20, 2013
Lambar Labari: 2513115

Kasar Turkiya Na daga Cikin Kasashen Da Suka Saka Kansu Cikin Rikici A yankin

Bangaren kasa, da dama daga masana kan harkokin yankin gabas ta tsakiya na ganin cewa gwamnatin Turkiya ta tabka babban kure bayan da ta bi sahun wasu daga cikin kasashen da suke yi Amurka da sauran kasashen yammacin turai amshin shata ayankin gabas ta tsakiya domin kare manufofin siyasar yahudawan sahyuniya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al'alam cewa, yanzu haka wasu da dama daga masana kan harkokin yankin gabas ta tsakiya na ganin cewa gwamnatin Turkiya ta tabka babban kure bayan da ta bi sahun wasu daga cikin kasashen da suke yi Amurka da sauran kasashen yammacin turai amshin shata ayankin gabas ta tsakiya.
A wani labarin kuma an tababtar da cewa an kai wasu tagwayen hare-hare a birnin Ankara na kasar Turkiya a daren jiya a kan babban ginin ma'akatar shari'a ta kasar da kuma ofishin jam'iyya mai mulki, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane biyu. Ministan shari'a na kasar ta Turkiya Sa'adullah Argin ya sheda cewa, an kai hare-haren ne kimanin karfe 9 na daren jiya, wanda ya lalata gaban babban ginin ma'aikatar tsaro, haka nan kuma an kai wani harin a kan babban ofishin jam'iyya mai mulki ta Justice and Development Party karkashin jagorancin Firayi ministan kasar Rajab Tayyib Ardugan.

Argin ya ce mutane biyu sun samu raunuka sakamakon hare-hare, kuma tuni jami'an tsaro suka fara gudanar da bincike kan lamarin. Kasar Turkiya dai ta kwashe tsawon sheku 31 tana fuskantar ayyukan tawaye daga kungiyar 'yan awaren kurdawa ta PKK, wadda kan dauki alhaki kai hare-hare a kan kaddarorin gwamnatin kasar, duk kuwa da cewa har yanzu babu wani mutu ko wata kungiya da ta dauki nauyin kai hare-haren. amma wadannan hare-haren na jiya sun zo ne a lokacin da gwamnatin kasar ta saka kanta cikin rikice-rikicen kasashen larabawa musamman ma rikicin kasar Syria, inda ta bude dukkanin iyakokinta da Syria dubban mayaka daga kasashen duniya domin su shiga cikin kasar Syria domin kai hare-hare.

1205900


captcha