Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Mahmud Alhabash ministan kula da harkokin addinin muslunci na hukumar cin gishin kan palastinawa ya yi Allawadai da akkakusar murya kan farmakin da yahudawan sahyuniya suka kai kan masallacin Qods mai alfarma tare da bayyana haka a matsiyin wuce dukkanin iyakoki da dokoki na kasa da kasa.
A bangare guda kuma kungiyar Gwagwarmaya ta Hamas ta nemi babbar Kotin Hukunta Leifi ta MDD da ta hukunta shugabanin haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin wadanda suka aikata laifukan yaki. A jiya talata ne Mr Izzaturrashk daya daga cikin manbobin Ofishin Siyasa na Kungiyar Hamas ya bayyana cewa har a bada Al’ummar yankin Palastinu ba zata manta ba da irin kisan kiyashin da aramtacciyar kasar Isra'ila take musu ba.
Kisa da wuce iyaka da aramtacciyar kasar Isra'ila take yi a kan Al’ummar Palastinu ba zai raunana Al’ummar ba ko kadan. Daga karshe Izzaturrashk ya kira Al’ummar Palastinu da su kara Dagewa da dauriya wajen yin gwagwarmaya da aramtacciyar kasar Isra'ila sannan ya kira ‘yan Kungiyar Gwagwarmaya ta hamas da su kara hada kansu wajen yin gwagwarmaya da aramtacciyar kasar Isra'ila sannan yayi godiya ta musamman ga Kungiyar Kasashen musulmi da Kungiyar Larabawa da Al’ummar Larabawa da na musulmi wajen goyan bayan da suke ba Al’ummar Palastinu.
1210489