Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da janazar bababn malamin addinin muslunci a yankin gabcin Saudiyya Ayatollah Abdulhadi Al-fadli wanda Allah yay i wa rasuwa bayan fama da rashin lafiya an kuma gudanar da janazar a garin Saihat da ke gabacin kasar tare da halartar dubban muminai daga cikin kasar da ma wajenta, musamman daga kasashen Iraki Kuwait Bahrain da sauransu.
A bangare guda kuma jagoran juyin juya halin musulunci ya fitar da bayanin ta’aziyya kan rasuwar malamin, inda yake cewa: Cikin tsananin bakin ciki da alhini na samu labarin rasuwar Allamah Ayatullah Dakta Abdulhadi al-Fadhli.
Wannan babban malami, ya gudanar da rayuwarsa madaukakiyya ce wajen jihadi na ilimi da siyasa da kuma ba da kariya ga ababe masu tsarki na al'ummar musulmi da kuma batutuwan da suka shafe su.
Marigayin ya kasance daga cikin masana da masu tunani na musulmi na gaba-gaba, babban dalilin da ke tabbatar da hakan kuwa shi ne irin rubuce-rubucensa masu kima da kuma sauran abubuwan da ya bari.
Marigayi Al-Fadhli ya kasance makomar malaman wannan al'umma, sannan kuma ta hanyar tunani da yunkuri da jihadi da kuma kokarinsa na hada kan musulmi ya kasance abin koyi wajen janyo hankula da zukatan al'ummar musulmi waje guda da kuma nesantar duk wani rikici da sabani a tsakaninsu sannan da kuma tinkarar babban makiyin da suka yi tarayya a kansa gaba dayansu.
Haka nan kuma a karshe-karshen rayuwarsa marigayin ya yi hakuri da wata jarabawa ta Ubangiji ta rashin lafiya da ya yi fama da ita, wanda hakan wata alama ce mai girman gaske ta wani mutum mumini mai hakuri da godiya sannan kuma mai yarda da Ubangiji Madaukakin Sarki da kuma dogaro da shi.
A saboda haka ne nake isar da sakon ta'aziyya ta ga iyalansa masu girma da abokai da dalibai da kuma masoyansa, musamman malaman al'ummar musulmi da kuma makarantar Hauza, sannan kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya saukar da rahamarsa ga wannan marigayin mai girma, ya sanya Aljanna ta zamanto ita ce makomarsa ta har abada, haka nan kuma ya sanya shi cikin yardarsa mai fadi, sannan kuma ya ba wa iyalansa da kuma masoyansa hakuri da juriyar wannan rashi. Kamar yadda kuma nake rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba wa dukkanin malamanmu masu girma cikakkiyar lafiya da kuma ci gaba da samun dacewar koyi da wannan marigayin a fagen tunani da halaye da jihadi.
1210825