IQNA

Idan Yunkurin Fadakar Musulmi Ya Wanzu Zai Iya Gurgunta Makircin Makiya Musulunci

13:46 - May 01, 2013
Lambar Labari: 2527081
Bangaren siyasa, a litinin da ta gabata ce jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya gabatar da jawabi a gaban taron malaman addinin muslunci da kuma fadakar al'ummar musulmi a birnin Tehran inda ya jaddada wajabcin yin tsayin daka a gaban makircin makiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cikakken bayanin nasa wanda ya farad a cewa; Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin su tabbata ta Shugabanmu Muhammad al-Mustafa tare da Alayensa tsarkaka da sahabbansa zababbu, da wadanda suka bi su da kyautata har zuwa ranar tashin kiyama.
Ina muku maraba da zuwa, Ya ku baki masu girma, sannan kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya sanya albarka cikin wannan kokari (da aka yi) sannan kuma ya sanya hakan ya zamanto mai tasiri wajen ci gaban al'ummar musulmi, "Lalle shi mai ji da kuma amincewa ne".
A yau maudhu'in 'farkawa ta Musulunci' wanda za ku yi magana da kuma bahasi kansa a wannan taron, ya kasance daga cikin lamurra na gaba-gaba a duniyar musulmi sannan a tsakanin al'ummar musulmi; haka nan kuma wani lamari ne mai ban mamaki wanda cikin yardar Allah idan ya tabbata da kuma ci gaba da wanzuwa, to nan ba da jimawa ba zai sake dawo da ci gaban Musulunci ga al'ummar musulmi da kuma duniya baki daya.
Abin da a halin yanzu muke ganinsa da idanuwanmu sannan kuma babu wani mutum da ya san inda aka sa gaba da zai yi inkarinsa, shi ne cewa a halin yanzu Musulunci ya fice daga yanayin zama dan kallo a fage na siyasa da zamantakewa ta duniya da komawa cikin fagen masu tasiri da ayyana makoma a duniya. Ya sami wani matsayi mai girma da kuma bayyanar da kansa a fage na rayuwa da siysa da gwamnati da kuma tsarin na zamantakewa, wanda hakan wani lamari ne mai matukar muhimmanci a irin wannan duniya da muke ciki bayan shan kashin tsarin gurguzu da na jari hujja. Wannan shi ne tasiri na farko da wadannan sauye-sauye na siyasa da juyin juya hali da suka faru a arewacin Afirka da kuma kasashen larabawa suka haifar a mahanga da kuma mizani na kasa da kasa. Hakan kuwa wani lamari da ke bishara da wani lamari mai girma da zai faru nan gaba.
Farkawa ta Musulunci wacce masu magana da yawun girman kan duniya da hukumomin da suka ci baya ba sa ko so a ambaci wannan kalma sannan kuma suna cikin tsoro a duk lokacin da suka ji an ambace ta, wata hakika ce wacce a halin yanzu a kusan dukkanin kasashen musulmi ana iya ganinta a fili. Mafi girman alamar hakan ita ce irin kumajin da al'umma musamman matasa suke nunawa wajen rayar da irin daukakar da Musulunci yake da ita, da kuma masaniyar da suka samu dangane da yanayin tsarin mulkin mallaka na duniya da kuma bayyanar bakar fuskar azzaluman gwamnatoci ma'abota girman kai da cibiyoyin da sama da shekaru dari biyu suka lankwame kasashen Musulunci da ma wadanda ba na musulmin ba da kuma ci gaba da zaluntar wadannan al'ummomi.
Bangarorin wannan farkawa mai albarka suna da girma sannan sun fadada. To amma irin nasarorin da aka samu a wasu kasashen arewacin Afirka, za su iya kwantar da hankula dangane da sakamako mai girma da za a samu a nan gaba. A koda yaushe cikan alkawarin Ubangiji lamari ne da ke sanya fata cikin zukata dangane da cika manyan alkawurra. Hikiyar da Alkur'ani mai girma ya kawo dangane da alkawarin Allah ga mahaifiyar Annabi Musa, daya ne daga cikin misalan da suke tabbatar da cika alkawarin Ubangiji.
A wancan lokacin mai wahalar gaske da aka saukar da umurnin jefa akwatin da ke dauke da wannan jariri (annabi Musa) cikin teku, Allah Madaukakin Sarki Ya yi (wa mahaifiyar Annabi Musa) alkawarin cewa: "Lalle ne Mu, Masu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Masu sanya shi ne a cikin Manzanni" (Suratul Kasas 28:7). Tabbatuwar alkawarin farko wanda alkawari ne mafi karanci sannan kuma mai faranta wa mahaifiya rai, alama ce ta tabbatuwar alkawari na manzanci, wanda wani lamari ne mai girma wanda kuma yake cike da wahalhalu da kokari da kuma hakuri. "Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa domin idanunta su yi sanyi, kuma ba za ta yi bakin ciki ba, kuma domin ta san cewa lalle alkawarin Allah gaskiya ne" (Suratul Kasas 28:13). Wannan alkawari na gaskiya, shi ne dai wannan manzanci wanda aka tabbatar da shi bayan wasu shekaru sannan kuma ya sauya yanayin tarihin duniya.
Wani misalin kuma na daban shi ne tunatarwa dangane da gagarumin karfin da Ubangiji yake da shi wajen gamawa da wadanda suka kawo wa Dakin Allah hari wanda Allah Madaukakin Sarki ya sanar da Manzon Allah ne don kadaitar da wadanda yake magana da su, inda yake cewa: "Saboda haka, sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka'abah) (Suratu Kuraish 106:3) sannan a wani wajen kuma yake cewa: "Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin bata ba" (Suratul Fil 105:2).
Ko kuma saboda karfafa ruhin Annabi abin kaunarsa da kuma tabbatar da alkawarinsa: "Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ki ka ba" (Suratud Duha 93:3) yana tunatar da ni'imomi masu ban mamaki "Ashe, bai same ka maraya ba, sa'an nan Ya yi maka makoma? Kuma Ya same ka marar shari'a, sai Ya shiryar da kai? (Suratud Duha 93:6-7). Akwai irin wadannan misalan cikin Alkur'ani mai girma da yawan gaske.
A lokacin da Musulunci ya yi nasara a Iran sannan kuma ya sami nasarar kwace tungar Amurka da sahyoniyawa a daya daga cikin yankuna masu muhimmanci na wannan yanki mai matukar muhimmanci, masu yawo da daukan darasi da hikima sun san cewa idan har aka yi hakuri da kuma amfani da basira, to kuwa za a ci gaba da samun nasarori daya bayan daya.
Hakikanin lamari mai ban mamaki da ya faru a Jamhuriyar Musulunci wanda hatta makiyanmu sun tabbatar da hakan, an sami dukkanin hakan ne albarkacin dogaro da alkawarin Ubangiji da hakuri da tsayin da ka da neman taimakon Ubangiji. A duk lokacin da mutane masu rauni, wadanda idan suka ga wata wahala, suke fadin cewa: "Lalle hakika, za a cim mana" (Suratush Shu'ara 26:61), nan take al'ummarmu sukan ce: "A'a, ko daya, (ba za su riske mu ba); hakika Ubangijina yana tare da ni, zai kuwa shiryar da ni (hanyar tsira)" (Suratush Shu'ara 26:61).
A yau dai wannan gagarumar kwarewar tana hannun wadannan al'ummomi wadanda suka yi tsayin daka a gaban ma'abota girman kai da 'yan mulkin mallaka, sannan kuma suka sami nasarar kawar da lalatattun hukumomi da 'yan amshin shatan Amurka ko kuma girgiza su. Tsayin daka da hakuri da basira da dogaro da alkawarin Ubangiji na cewa: "Kuma lalle, hakika, Allah Yana taimakon wanda yake taimakonSa. Lalle Allah, hakika, Mai karfi, Mabuwayi ne" (Suratul Hajj 22:40) zai iya bude wa al'ummar musulmi wannan tafarki abin alfahari har zuwa ga kololuwar inda ake son kai wa gare shi.
A halin yanzu a wannan taron mai muhimmanci da wasu gungun malaman al'umma daga kasashe da kuma mazhabobi daban-daban da suka taru, ina ganin ya dace in yi bayanin wasu batutuwa na wajibi da suka shafi farkawa ta Musulunci:
Batu na farko shi ne cewa a mafi yawan lokuta malamai da masu gyara na addini ne suka faro guguwar farkawar da ta faru a kasashen wannan yankin a daidai lokacin da ‘yan mulkin mallaka suka fara bayyana. Ko shakka babu sunayen jagorori da fitattun mutane irin su Sayyid Jamaluddeen da Muhammad Abdu da Mirza Shirazi da Akhund Khorasani da Mahmud Al-Hasan da Muhammad Ali da Sheikh Fadhlullah da Hajj Agha Nurullah da Abul A'ala Maududi da sauran fitattun malamai da mujahidai da yawa da suka fito daga kasashen Iran da Masar da Ingiya da Iraki, sun shiga cikin tarihi. A wannan zamani na mu ma fitaccen suna mai haskakawa na Imam Khumaini mai girma ya kasance tamkar wani haske ne mai haskaka tarihin juyin juya halin Musulunci. A wannan fagen akwai daruruwan sanannun malamai da wadanda ba a sansu ba da a yau da kuma jiya suka taka gagarumar rawa a yunkurin gyara da suka faru a kasashe daban-daban. Lalle jerin sunayen masu gyara na addini daga mutanen da ba malamai ba irin su Hasan al-Banna da Ikbal Lahori suna da yawa sannan da ban mamaki.
Malamai da masanan addini a dukkanin kasashe sun kasance wata madogara abar komawar mutane a bangaren tunani da hakuri da kuma karfafa ruhi. A duk lokacin da aka sami faruwar wani sauyi, malaman sun taka rawar masu shiryarwa, haka nan kuma sun kasance a cikin sahu na mutane wajen fuskantar hatsari. Alaka ta tunani a tsakaninsu da mutane ta karu sannan kuma shiryarwarsu ta yi tasirin gaske wajen fahimtar da al'umma inda aka sa a gaba. Kamar yadda hakan ya zamanto mai albarka da kuma amfani ga yunkurin farkawa ta Musulunci, haka nan kuma suka zamanto babbar matsala ga makiyan al'umma da masu kulla makirce makirce ga Musulunci da kuma masu adawa da tabbatar da iko da hukuma ta Musulunci. Don haka suka matsa kaimi wajen ganin sun kawar da wannan madogara ta tunani daga sansani na addini da kuma samar da wasu sabbin mutane wadanda suka fahimci cewa ana iya kulla yarjejeniya da su wajen cutar da koyarwa da ababe masu kima na addini. Hakan kuwa bai taba faruwa da malamai da masu riko da addini masu takawa ba, kuma a nan gaba ma ba zai faru ba.
Hakan yana kara irin nauyin da ke wuyan malamai. Wajibi ne ta hanyar taka tsantsan da kuma sanya ido sosai, sannan kuma ta hanyar fahimtar irin makirce-makircen makiya, su rufe dukkanin wata kafar da makiya za su sami damar kutsawa da kuma hana su samun nasara. Neman jin dadin duniya babban bala'i ne. Gurbata da kuma yaudaruwa da kyautar masu mulki na duniya da dawagitan shugabanni, lamari ne mai hatsarin gaske da ke raba malamai da mutane da kuma irin yardar da take tsakaninsu. Kwadayi da neman mulki wadanda abubuwa ne da suke sanya komawa ga masu mulki, abubuwa ne masu hatsarin gaske da suke gurbata mutum da kai shi zuwa ga fasadi da kauce wa hanya. Wajibi ne a koda yaushe su dinga tuna wannan ayar mai girma: "Wancan gidan Lahira Muna sanya shi ga wadanda suke ba su nufin daukaka a cikin rayuwar duniya, kuma ba su son barna. Kuma akiba ga masu takawa take" (Suratul Kasas 28:83).
A halin yanzu a wannan zamani na yunkuri mai sanya fata na farkawa ta Musulunci, a wasu lokuta a kan ga wasu yunkuri da ke nuni da kokarin ‘yan amshin shatan Amurka da sahyoniyawa wajen samar da wasu madogaran maras aminci, sannan a daya bangaren kuma ga wasu ‘Yan Karuna masu bautar son zukatansu na kokarin janyo ma'abota addini da tsoron Allah zuwa ga tabarmarsu da ke cike da guba. A saboda haka wajibi ne malaman addini da sauran masu riko da addini su yi gagarumin taka tsantsan.
Batu na biyu shi ne wajibcin tsara manufa ta tsawon lokaci ga wannan farkawa ta Musulunci da ke faruwa a kasashen musulmi; wato kololuwar manufar da za ta tsara wannan farkawa da kuma taimakawa al'umma isa ga wani matsayi. Ta hanyar fahimtar hakan ne za a iya tsara wata taswirar hanya da kuma tsara manufofi na tsaka-tsaki da kuma na kurkusa. Manufa ta karshen kuwa ba za ta taba zama wani abu kasa da ‘samar da ci gaba da kuma al'adu na Musulunci masu haskakawa' ba. Wajibi ne al'ummar musulmi da dukkanin bangarorinsu su kai ga irin ci gaba da Alkur'ani yake son su kai gare shi. Siffa ta asali kuma ta gaba daya ta irin wannan ci gaban kuwa ita ce dukkanin al'umma su amfana da dukkanin fagage na duniya da na lahira wanda Allah Madaukakin Sarki ya samar da su don tabbatar da sa'ada da daukakar mutane a wannan duniya. Ana iya ganin zahirin irin wannan ci gaba ne cikin hukuma ta mutane, cikin dokokin da aka samo su daga Alkur'ani mai girma, cikin kokari da biyan bukatun bil'adama, cikin nesantar koma baya da bidi'oi, cikin samar da jin dadi da dukiya ta gaba daya, cikin tabbatar da adalci, cikin ‘yantuwa daga tattalin arzikin da ya ginu bisa cin riba da zaluntar mutane, cikin yada kyawawan halaye, cikin goyon bayan wadanda aka zalunta, da kuma kokari aiwatar da aiki da sabbin abubuwa. Daga cikin laziman wannan gini na ci gaba har da dubi irin na ilimi da kwarewa cikin fagage daban-daban, kama daga ilmummuka zuwa ga tsarin koyarwa da tarbiyya, haka nan kuma daga tattalin arziki da ayyukan bankuna zuwa ga samar da kayayyakin da ake bukata da kuma fasaha, haka nan kuma daga kafafen watsa labarai na zamani har zuwa ga fasaha da fina-finai da kuma alaka ta kasa da kasa da sauransu. Dukkanin wadannan suna daga cikin bukatu na wannan ci gaban.
Kwarewar da muke da ita ta tabbatar da cewa dukkanin wadannan abubuwan, abubuwa ne masu yiyuwa kuma ba za su fi karfin al'ummarmu ba. Bai kamata a dinga yi wa irin wannan yanayi wani kallo na yanke kauna da jin cewa ba za a iya ba. Mummunan zato ga irin karfin da ake da shi, kafirce wa ni'imar Ubangiji ne; sannan kuma gafala ce daga taimako na Ubangiji da kuma fadawa cikin tarkon zamiya. "masu zaton mugun zato game da Allah" (Suratul Fath 48:6). Muna iya kawo karshen mallake komai da ‘yan mulkin mallaka suka yi a fagagen ilimi da tattalin arziki da siyasa, da kuma ciyar da al'ummar musulmi gaba da tabbatar da hakkokin mafiya yawan al'ummomin duniya wadanda a halin yanzu suka zamanto karkashin zalunci wasu ‘yan tsiraru.
Batu na uku shi ne cewa cikin yunkuri na farkawa ta Musulunci, wajibi ne a koda yaushe a dinga lura da irin cutarwar da aka fuskanta sakamakon koyi da kuma biyayya ga kasashen yammaci cikin siyasa da halaye da kuma salon rayuwa. Sama da karni guda kenan kasashen musulmi suke fuskantar bala'oi masu halakarwa irin su dogaro da kaskanci na siyasa, talauci da rashi na tattalin arziki, munanan halaye da dabi'u, koma baya a fagen ilimi sakamakon biyayya da kuma koyi da al'adu da siyasar gwamnatocin girman kai na duniya, alhali kuwa al'ummar musulmi sun kasance masu gagarumin ci gaba abin alfahari a dukkanin wadannan fagagen.
Bai kamata a dauki wadannan maganganu a matsayin adawa da kasashen yammaci ba. Mu dai ba ma kiyayya da wani mutum saboda yankin da ya fito. Mun koya daga Imam Ali (a.s) wanda ya siffanta mutum da cewa: ‘imma dai dan'uwanka ne a addini, ko kuma kwatankwacinka cikin halitta". Korafin da muke yi dangane da zalunci da girman kai da iko da wuce gona da iri, da fasadi da munanan halaye da ayyuka wadanda ‘yan mulkin mallaka da ma'abota girman kai suka haifar wa al'ummomi ne. A halin yanzu muna iya ganin tsoma baki da tursasawar da Amurka da wasu ‘yan amshin shatanta a wannan yankin suke yi cikin lamurran kasashen da iskar wannan farkawar ta kada ta kuma haifar da yunkuri da kuma juyin juya hali.
Bai kamata a bari alkawurra da kuma barazanar da suke yi su yi tasiri cikin matsaya da kuma ayyuka na siyasa da kuma gagarumin yunkuri na mutane ba. A nan ma wajibi ne mu dau darasi daga irin kwarewar da ake da ita. Wadanda shekaru aru-aru suka damfara dukkanin fatansu ga alkawurran Amurka da kuma dogaro da azzaluman shugabanni, sun gagara magance koda guda daga cikin matsalolin da al'ummominsu suke fuskanta ko kuma su magance wani zalunci da ake musu ko kuma wa wasunsu ba. Wadannan mutane ta hanyar mika wuya ga Amurkan da suke yi, sun gagara koda hana rusa gida guda ne daga cikin gidajen Palastinawa a kasar da take ta Palastinawa ce. ‘Yan siyasa da masanan da suka fada tarkon alkawurra ko kuma barazanar ma'abota girman kai sannan kuma suka rasa gagarumar dama ta farkawa ta Musulunci da ta kunno kai, wajibi ne su ji tsoron barazana ta Ubangiji da ke cewa: "Shin, ba ka lura ba da wadanda suka musanya ni'imar Allah da kafirci, kuma suka saukar da mutanensu a gidan halaka. Suna konuwa a wutar Jahannama, kuma tir da matabbatarsu" (Suratu Ibrahim 14:28-29).
Batu na hudu shi ne cewa a yau daya daga cikin mafiya hatsarin abubuwan da suke barazana ga farkawa ta Musulunci, shi ne kokarin haifar da rarrabuwa da kuma mayar da wannan yunkurin zuwa ga wani yunkuri na adawa da zubar da jini na kungiyanci da mazhaba da kabilanci da ‘yan kasanci. A halin yanzu kungiyoyin leken asirin kasashen yammaci da sahyoniyawa ta hanyar taimakon dalolin (kudaden) man fetur da ‘yan siyasa da suka sayar da kansu, tun daga gabashin Asiya har zuwa arewacin Afirka musamman a kasashen larabawa, suna ci gaba da aiwatar da wannan makirci da kuma ba shi dukkanin muhimmanci. Ana ta amfani da kudaden da za a iya amfani da su wajen faranta wa bayin Allah zukata, amma sai ana amfani da su wajen barazana ga rayuwarsu, kafirta mutane da gudanar da ayyukan ta'addanci da dana bama-bamai da zubar da jinin musulmi da kuma ruruta wutar kiyayya da gaba. Wadannan mutane da suke ganin hadin kan al'ummar musulmi a matsayin barazana ga bakaken manufofinsu, suna ganin rarraba kan al'ummar musulmi a matsayin mafi saukin hanyar isa ga wannan manufa ta su ta shaidanci. Suna amfani da bambancin mahanga a fagen fikihu da akida da tarihi da hadisi da ake da shi - wanda kuma wata dabi'a ce da ba za a iya guje mata ba - wajen kafirta musulmi da zubar da jininsu da kuma haifar da fitina da fasadi a tsakaninsu.
Dubi da idon basira cikin irin rikice-rikice na cikin gida da ke faruwa a kasashen musulmi, a fili zai iya bayyanar da hannayen makiya cikin hakan. Ko shakka babu wadannan hannaye masu zubar da jini, suna amfana ne da irin jahilci da bakar aniya da karancin fahimta da ke a tsakaninmu, sannan kuma suke amfani da hakan wajen ruruta wannan wutar. Nauyin da ke wuyan masu kawo gyara da masana na addini da siyasa a wannan fagen nauyi ne mai girman gaske.
A halin yanzu kasar Libiya ta wani bangare, Masar da tunusiya ta wani bangaren, Siriya ta wani bangaren, Pakistan ta wani bangaren, Iraki da Labanon ta wani bangaren na daban, suna fada cikin wannan wutar (ta fitina) da aka hura. Wajibi ne a lura sosai sannan kuma a nemi hanyar magance hakan. Karamin tunani ne a jingina dukkanin wadannan abubuwa ga akida da kabilanci. Kafafen watsa labaran kasashen yammaci da na yankin nan ‘yan amshin shata, suna bayyana yaki mai ruguzarwar da ke faruwa a kasar Siriya a matsayin wani rikici na Shi'a da Sunna, don share fagen tabbatar da tsaro ga sahyoniyawa da makiyan gwagwarmaya a kasar Siriya da Labanon. Alhali kuwa bangarori biyun da suke rikici a kasar Siriya, ba Sunna ba ne, ba kuma Shi'a ba ne, face dai masu goyon bayan gwagwarmayar fada da sahyoniyawa da kuma masu adawa da su ne. Gwamnatin Siriya ba wata gwamnati ce ta Shi'a ba, haka nan su ma ‘yan adawan da babu ruwansu da addini sannan kuma masu adawa da Musulunci ba ‘yan Sunna ba ne. Nasarar da wadanda suka rura wannan wutar mai cutarwa suka samu ita ce sun sami nasarar motsa zukatan wasu masu kananan kwakwalwa ta hanyar amfani da mazhaba. Idan aka dubi wannan fage ta bangarori daban-daban, hakikanin lamarin ya kan iya fitowa fili ga duk wani mutum mai adalci.
Dangane da kasar Bahrain kuwa, irin farfagandar da ake yadawa wata hanya ce ta karya da wasa da hankulan mutane. A Bahrain, mafi yawan al'ummar kasar da ake zalunta wadanda shekara da shekaru kenan aka haramta musu hatta hakkin kada kuri'a da sauran hakkoki na ‘yan kasa sun mike ne saboda neman wannan hakki na su na gaskiya. To amma shin ya dace a bayyana wannan rikicin a matsayin rikicin Shi'a da Sunna don kawai mafi yawan wadannan mutanen ‘yan Shi'a ne, sannan kuma hukuma mai mulki a can wacce ba ruwanta da addini amma take nuna cewa ita ‘yar Sunna ce? ‘Yan mulkin mallaka na kasashen Turai da Amurka da kawayensu a wannan yankin suna son su nuna hakan, to amma shin hakan gaskiya ce?
Hakan lamari ne da ke sanya malaman addini da masu son kawo gyara su yi tunani da kuma jin cewa lalle akwai wani nauyi a wuyansu da kuma fahimtar manufofin makiya cikin kambama sabani na mazhana da kabila da kungiyanci da ake da shi.
Batu na biyar shi ne cewa daya daga cikin hanyoyin tabbatar da cewa yunkurin farkawa ta Musulunci yana kan tafarki madaidaici (ko a'a) shi ne cewa wajibi ne a lura da matsaya da mahangar wannan yunkurin kan batun Palastinu. Tun daga shekaru 60 din da suka gabata zuwa yanzu babu wani abin da ke sosa ran al'ummar musulmi kamar yadda mamaye kasar Palastinu yake sosa musu. Wannan matsala ta Paalstinu tun daga ranar farko har zuwa yau din nan, babu wani abin da suka gani in banda kisan gilla, kashe mutane, rusa gidaje da mamaya da kuma wuce gona da iri kan ababe masu tsarki na Musulunci. Tsayin daka da gwagwarmayar tinkarar makiya, wani lamari ne da dukkanin mazhabobin Musulunci suka yi tarayya kansa. Duk wani yunkuri a kasashen musulmi da ya yi watsi da wannan nauyi na addini da kuma kasa sannan kuma bisa bukatar Amurka da kuma riko da wasu hujjoji da suka saba wa hankali da hikima ya mance da wannan batu na Palastinu, bai kamata ya yi zaton cewa za a kalle shi kallo irin na mai sadaukarwa ga Musulunci da kuma daukansa a matsayin aboki ba. Wannan wani mafari ne. Duk wanda bai amince da taken ‘yanto masallacin Kudus mai girma ba da kuma ‘yantar da al'ummar Palastinu da kasar Palastinu ba, ko kuma ya mayar da hakan a matsayin wani abu na bayan fage da kuma juya wa kungiyoyin gwagwarmya baya, to abin tuhuma ne. Wajibi ne al'ummar musulmi a ko ina sannan kuma a kowane lokaci su sanya wannan mizanin a matsayin tushe na ayyukansa sannan kuma abin lura.
Ya ku baki abin kauna! ‘Yan'uwa maza da mata!....
Kada ku kawar da idanuwanku daga makirce-makircen makiya; don kuwa gafalarmu za ta zamanto wata dama ce ga makiya.
Hakika darasin Imam Ali (a.s) a gare mu shi ne cewa: 'Duk wanda ya yi barci, ba za a yi barci saboda shi ba'. Kwarewar da muke da ita a Jamhuriyar Musulunci wata kwarewa ce da take cike da abubuwan daukan darasi a wannan bangaren. Tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, tun daga lokacin gwamnatocin kasashen yammaci da Amurka ma'abociyar girman kai, wacce take iko da dawagitan Iran da kuma iko da fagen siyasa da tatalin arziki da al'adu na kasar nan, sannan kuma ta yi sako-sako da gagarumin karfi na Musulunci da ke tattare da al'umma da kuma gafala da irin karfin Musulunci da Alkur'ani mai girma, suka fahimci matsalar da suka fada cikinta sakamakon wannan gafala da suka yi. Don haka suka shigo da dukkanin karfinsu na siyasa da leken asiri wajen cike wannan hasara da suka fuskanta.
Tsawon wadannan shekaru talatin da wani abun mun shaidi makirce-makirce kala-kala da suka kulla mana. To sai dai a hakikanin gaskiya akwai abubuwa guda biyu da suka sanya wadannan makirce-makirce na su suka zamanto aikin baban giwa, su ne: riko da koyarwa ta addini da kuma kasantuwar al'umma a fage.
Wadannan abubuwa su ne mabudin magance matsaloli a ko ina. Abin da ke tabbatar da abu na farkon shi ne imani da kuma gaskata alkawarin Ubangiji, sannan abin da ke tabbatar da na biyun shi ne kokari tare da tsarkin zuciya da kuma gaskiya. Al'ummar da ta yi amanna da gaskiyar shugabanninta da kuma ikhlasinsu, to kuwa za ta motsar da fagen da ake ciki ta hanyar wannan kasantuwa ta su mai albarka. A duk inda al'umma suka shigo fage da tsayayyiyar azama, to kuwa babu wani karfin da zai iya da su. Wannan wata kwarewa ce mai haifar da nasara ga dukkanin al'ummomin da suka haifar da farkawa ta Musulunci ta hanyar kasantuwarsu a fage.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya tabbatar muku da kuma dukkanin al'ummar musulmi shiriya, taimako da kuma rahamarsa.

1219899
















captcha