Kamfanin dillancin labaran iqna ya habrta cewa, da dama da cikin masana sun yi imanin cewa an kirkiro rikicin kasar Syria ne da nufin raunana gwagwarmayar al'ummar yankin wadanda suke hankoron ganin sun kawo karshen zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma mamayarta kan yankunan al'ummomin palastinu da ma sauran yankunan musulmi da na larabawa.
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya gargadin cewa daukar duk wasu matakai da suka yi hannun riga da dokoki na kasa da kasa kan sha'anin Syriya, hakan zai kara rura wutar rikicin da ake fama da shi a kasar ne, wanda kuma zai shafi sauran kasashe da ke yankin. Shugaba Ptin ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake ganawa da Firayi ministan Haramtacciyar Kasar Isra'ila Benyamin Natanyahu, wanda ya isa kasar Rasha a jiya da nufin gamsar da mahukuntan kasar, da su janye batun bayar da makamai masu linzami samfurin S-300 ga gwamnatin kasar Syria.
A lokacin ganawar ta su dai shugaba Putin ya jaddada wa Natanyaho cewa, Rasha ba za ta amince da duk wani mataklin tsokana da zai kara dagula lamurra a Syria ba, yana mai ishara da hare-haren da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan Syria a kwanakin da suka gabata. A wata zantawa da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yi da manzon musamman na majalisar dinikin duniya kan rikicin Syria Lakhdar Ibrahim ta hanyar wayar tarho, Lavrov ya jaddada matsayin gwamnatin Rasha, kan cewa dole ne a warware rikicin Syria ta hanyar lumana tsakanin dukaknin bangarorin siyasar kasar.
1228549