Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jagora cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan bikin, Jagoran ya isar da sakon murnar wannan rana mai girma ga dukkanin al'ummar musulmi na duniya inda ya ce mafi muhimmancin nauyin da ke wuyan al'ummar musulmi a irin yanayin da ake ciki a halin yanzu shi ne taka tsantsan da fahimtar tafarkin da suka rika bugu da kari kan makirce-makircen da makiya suke kulla musu. Jagoran ya ci gaba da cewa: Babbar manufar makiya a halin yanzu ita ce haifar da sabani da rikici tsakanin musulmi. A saboda haka hadin kai da aiki tare shi ne mafi girman bukatar da duniyar musulmi take da ita a halin yanzu.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin makirce-makircen da makiya suka ta kulla wa Manzannin Allah da kuma sakonsu na kira zuwa ga gaskiya da suka zo da su, Jagoran cewa ya yi: irin wadannan makirce-makirce da adawa na makiya sun fi girma da tsanani a kan sakon Manzon Allah (s.a.w.a), sannan kuma sun ci gaba da yin hakan har zuwa karshen rayuwarsa mai albarka.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da cewa har ya zuwa yau din nan makiyan suna ci gaba da nuna wannan kiyayya da adawarsu ga sakon Musuluncin, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Sakamakon gazawar da sauran sakonni wadanda ba na Ubangiji ba irin su akidar markisanci wajen tabbatar da sa'ada ga bil'adama, don haka a halin yanzu dukkanin zukata da fata sun koma ne ga addinin Musulunci. A saboda haka ne irin kiyayyar da ake yi wa addinin Musulunci a matsayin tafarkin da ke tabbatar da karama da adalci na Ubangiji ya kara tsananta.
Ayatullah Khamenei ya bayyana irin cin mutumcin Manzon Allah (s.a.w.a) da ake yi a halin yanzu a matsayin daya daga cikin misalan irin wadannan kiyayyar da ake nuna wa addinin Musuluncin, inda ya ce: Babu yadda za a iya yarda da cewa cibiyoyi da kungiyoyin leken asirin manyan kasashen duniya ba su da hannu cikin tsarawa da kuma goyon bayan irin wannan cin mutumcin Musulunci da kuma kiyayyar da ake nuna masa.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da cewa wasu daga cikin dabi'u da halayen musulmi sun taimaka wajen share fagen irin kiyayyar da ake nuna wa Musulunci a wasu bangarorin na duniya, Jagoran cewa ya yi: Wajibi ne musulmi su bayyanar da koyarwar Musulunci yadda take cikin dukkanin jaruntak da kuma gaskiya, don janyo hankulan sauran al'ummomi zuwa ga Musulunci.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wajibi ne musulmi su tsaya kyam wajen tinkarar irin kiyayyar da ake nuna wa sakon Musulunci, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a) da sauran muminai suka tsaya kyam tsawon tarihi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana basira da kuma fahimtar koyarwar Musulunci da kuma makirce-makircen da makiya suke kulla wa Musulunci da musulmi a matsayin lamurra masu tsananin muhimmanci wadanda kuma suka zamanto na wajibi inda ya ce: Babban makircin makiya shi ne haifar da sabani tsakanin musulmi da kuma haifar da rikici na mazhaba a tsakaninsu, don su kawar da musulmin daga asalin makiyansu, wato lalatattun ‘yan jari hujja da sahyoniyawa ‘yan fashin kasa sannan kuma marasa imani.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne al'ummar musulmi da suka hada da al'ummomi, ‘yan siyasa da masanansu, su fahimci irin wadannan makirce-makirce na makiya don su sami damar yin tunanin hanyoyin da za su yi fada da hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Abin da masu takama da karfi na duniya suke son cimmawa ta hanyar haifar da sabani tsakanin musulmin shi ne su kawar da su daga asalin batutuwan da suka fi damunsu da kuma haramta musu irin ci gaban da ya kamata a ce suna da su.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A baya dai ‘yan kasashen yammaci suna amfani da hanyar mulkin mallaka ne wajen cimma wannan manufa da suke da ita, to amma a halin yanzu suna amfani da hanyar haifar da sabani tsakanin musulmin ne wajen cimma wannan manufar.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Tabbas ‘yan kasashen yammaci ba za su iya goge wannan bakin fenti na mulkin mallaka daga fuskokinsu ta hanyar rera taken goyon bayan hakkokin bil'adama da demokradiyya ba.
Daga karshe dai Jagoran ya bayyana cewar: Bisa la'akari da wannan makirci na makiyan, wajibi ne musulmi, ta hanyar basira da fahimtar makirce-makircen makiya, su tsara na su hanyar fada da hakan wadda ita ce hanyar tabbatar da hadin kai, fahimtar juna da kuma aiki tare a tsakaninsu.
A farkon wannan taron dai wanda ya sami halartar dukkanin shugabannin bangarori uku na gwamnatin Iran, (shugaban kasa, shugaban majalisa da kuma shugaban ma'aikatar shari'a), da kuma shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin Musulunci, shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya gabatar da jawabinsa inda ya isar da sakon taya murnar wannan rana mai girma ga al'ummar Iran da sauran al'ummar musulmi na duniya. Shugaba Ahmadinejad ya bayyana Manzon Allah (s.a.w.a) a matsayin wata matattara ta ilimi da sirrukan Ubangiji. Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da irin siffofin da Annabi (s.a.w.a) ya kebanta da su, shugaban na Iran cewa ya yi: Asalin sakon Annabi Muhammad al-Mustafa (s.a.w.a) shi ne shiryar da bil'adama. A saboda haka ne ya fuskanci matsaloli da wahalhalu daban-daban.
Shugaba Ahmadinejad ya ci gaba da cewa: Manufar sakon Annabin Musulunci (s.a.w.a) ita ce tabbatar da kyawawan halaye a tsakanin dukkanin bil'adama.
Shugaban kasar ta Iran ya bayyana juyin juya halin Musulunci na kasar Iran karkashin jagorancin marigayi Imam Khumani a matsayin kira zuwa ga wannan sako na annabawan Allah inda ya ce: Tabbatar da tauhidi da adalci a duk fadin duniya kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari zai tabbata ne a lokacin bayyanar Imam Mahdi (a.s).
1238871