IQNA

18:02 - June 15, 2013
Lambar Labari: 2547445

Mutanen Iran Sun Ba Marada Kunya Ta Hanyar Fitowa Yayin Zaben Kasar

Bangaren siyasa, Rahotannin da suke fitowa daga bangarori daban-daban na Iran suna nuni da cewa al’ummar kasar sun amsa kiran Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da kuma bada wa makiyansu kasa a ido ta hanyar fitowa kwansu da kwarkwatansu a yayin zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisar kananan hukumomi da ake ci gaba da gudanarwa lamarin da ya sanya ma’aikatar cikin gidan kasar kara wa’adin lokacin kada kuri’ar da sa’oi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da kuma bada wa makiyansu kasa a ido ta hanyar fitowa kwansu da kwarkwatansu a yayin zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisar kananan hukumomi da ake ci gaba da gudanarwa lamarin da ya sanya ma’aikatar cikin gidan kasar kara wa’adin lokacin kada kuri’ar da sa’oi.
Rahotanannin sun ce, duk da kokarin da kafafen watsa labaran kasashen yammaci irin su Amurka da Birtaniya da sauransu suka yi na kashe gwiwan al’ummar Iran din da hana su fitowa kada kuri’un na su sai dai kuma al’ummar sun fito don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci na kasar da kuma taka rawar da tsarin ya ba su damar takawa wajen ayyana makomarsu.
Kasashen yammacin dai musamman Amurka ta yi amfani da takunkumin da ta sanya wa Iran da kuma matsin lamba na tattalin arziki da ta sanya al’ummar Iran din ciki wajen kashe musu gwiwa, to amma al’ummar Iran din sun fito don nuna matsayarsu na adawa da tsoma bakin duk wani dan waje cikin lamurransu ta cikin gida.
Ma’aikatar cikin gida da sauran cibiyoyi masu sanya ido kan zaben bugu da kari kan sauran cibiyoyin tsaron sun bayyana cewar babu wani abin da ya faru da zai iya zama barazana ga zaman lafiyar kasar ko kuma ingancin zaben sabanin abin da makiyan suka yi fatan gani a kasar.
1242774







captcha