IQNA

Jami'ar Azhar ta yi kira da a dauki matakan hana barkewar rikici a Masar

0:02 - June 30, 2013
Lambar Labari: 2553672
Bangaren kasa da kasa, babbar jami'ar musulunci ta kasar Masar Azhar ta yi kira da a dauki matakan hana barkewar rikici a kasar wanda idan har ya kasance to zai jawo yakin basasa da zai shafi kowa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, magoya bayan shugaban kasar Masar da kuma masu adawa da shi ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Alkahira da ma wasu biranan kasar a jiya, inda lamarin da ya kai ga yin taho-mu-gama a wasu yankuna tsakanin bangarorin biyu, inda aka tabbatar da mutuwar mutane 3 da suka hada da wani ba'amurke, wasu da dama kuma suka samu raunuka.

A birnin Alkahira dubban magoya bayan Mohammad Morsi sun taru ne a masallacin Rabi'at Adwiyyah, inda suka yi ta rera taken nuna goyon bayansu gare shi, tare da sukar masu adawa da shi, yayin da dubban masu adawa da Morsin kuma suka taru a dandalin Tahrir, wasu kuma suka taru a kofar fadar shugaban kasa da ke yankin Ittihadiyyaha cikin birnin na Alkahira, inda suke kira ga Morsi da ya gaggauta safka.

Domin abin da suka kira gazawarsa a dukkanin bangarori tun bayan da ya karbi shugabancin kasa shekara guda da ta gabata, tare da killace mukamai da dukakin harkokin gudanarwa a kasar ga 'yan kungiyar 'yan uawa musulmi kawai, sauran mutane kuma sun zama 'yan kallo, yayin da wasunsu kuma suke bayyana Morsi da kungiyar 'yan uwa musulmi a matsayin wadanda suka sace juyin juya halin da al'ummar kasar suka yi a kan gwamnatin Husni Mubarak, inda Morsi da kungiyarsa suka kafa wata gwamnatin da bata da bambanci da ta Husni Mubarak.

1249413



captcha