IQNA

'Yan ta'addan Syria suna harba makamai kan yankunan 'yan shi'a

23:57 - July 07, 2013
Lambar Labari: 2557826
Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin wahabiyanci da ke gudanar da ayyukan ta'addanci a cikin kasar suna ci gaba da kaddamar da hare-hare kan yankunan mabiya tafarkin yalan gidan manzon Allah da suke cikin gundumar Halab.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, 'yan ta'adda mabiya tafarkin wahabiyanci da ke gudanar da ayyukan ta'addanci a cikin kasar suna ci gaba da kaddamar da hare-hare kan yankunan mabiya tafarkin yalan gidan manzon Allah da suke cikin gundumar Halab da kewayenta.

A wani labarin kuma rahotanni daga kasar Syria na nuni da cewa sojojin kasar na ci gaba da kwace iko da yankuna da dama da a da 'yan bindiga suka kwace iko da su tare da kafa tungarsu. Dan rahoton tashar Al'alam a kasar Syria ya habarta cewa, sojojin na Syria suna ci gaba da nausawa a cikin yankunan da ke cikin gundumomin Homs da kuma Aleppo, inda suke fatattakar 'yan bindiga, inda a suka kashe adadi mai yawa a cikin makonni biyu da suka gabata, wasu kuma suka mika kansu da makaman da ke hannunsu.

Rundunar sojin kasar Syria ta sanar da gano wata maboyar 'yan bindiga a yankin Lazikiyyah, wadanda suke gudanar da ayyukan soji na hadin gwiwa tare da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila, kuma yanzu haka daruruwan sojoji sun killace wurin, tare da yin kira ga daukacin 'yan bindigar da su ajiye makaman da ke hannunsu su mika kansu, kafin daukar mataki na gaba a kansu.

1253642


















captcha