IQNA

Kawar da Morsi a Masar juyin juya hali ne ko kuwa juyin mulkin soji

13:51 - July 11, 2013
Lambar Labari: 2559893
Bangaren kasa da kasam da dama daga cikin masana suna ganin cewa kawar da Muhammad Morsi daga shugabancin kasar Masar sakamko ne na gazawar kungiyar yan uwa musulmi a lokacin da suka karbi shugabanin kasar da bai wuce shekara guda ba wanda soojoi suka yi amfani da hakan domin kawar da su.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, wasu daga cikin masana suna ganin cewa kawar da Muhammad Morsi daga shugabancin kasar Masar sakamko ne na gazawar kungiyar yan uwa musulmi a lokacin da suka karbi shugabanin kasar da bai wuce shekara guda ba wanda soojoi suka yi amfani da hakan domin kawar da su daga mulkin baki daya.

A wani labarin kuma Firayi ministan rikon kwaryar kasar Masar Hazim Al-bilawi ya bayyana aniyarsa ta kafa gwamnati da za ta kunshi ministoci da za su yi aiki ga al'ummar kasar Masar a cikin dan takaitaccen wa'adi na rikon kwarya, ba tare da yin la'akari da jam'iyu ko kungiyoyinsu ba.

Jaridar Almisri Al-yaum ta fadi a shafin na yanar gizo a yau Alhamis cewa, ta nakalto daga Hazim Albilawi cewa, bai yi magana da wata jam'iyyar siyasa ba dangane da batun kafa gwamnati, kuma ba zai yi magana da wata jam'iyya kan hakan ba, domin kuwa a cewarsa zai kafa gwamnati ne kawai tare da mutane bisa cancantarsu da gogewarsu, ba tare da la'akari da jam'iyyunsu ba.

Jam'iyyar 'yanci da adalci ta kungiyar 'yan uwa musulmi ta shelanta cewa ba za ta shiga cikin gwamnatin da Hazim Albilawi zai kafa ba ko da kuwa ya bukaci hakan, domin kuwa a cewar jam'iyyar sabon shugabancin kasar ba halastacce ba ne.

A bangare guda kuma wasu rahotanni daga kasar ta Masar sun ce wani babban kwamandan askarawan kasar ya tsallake rijiya ta baya a safiyar yau, bayan da wasu 'yan bindiga suka kai masa hari a yankin Sina'a.

1255767
captcha