IQNA

An Yi Allawadai da harin da magoya bayan kungiyar yan uwa musulmi suka kai a Mansurah

0:03 - July 22, 2013
Lambar Labari: 2564839
Bangaren kasa da kasa, an yi Allawadai da harin da magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi suka kai a mansura a kasar Masar kan jami'an tsaro sinda suka kashe uku daga cikin jami'an tsaron kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakato daga shafin sadarwa na kamfanin dilalncin labaran masar cewa, an yi Allawadai da harin da magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi suka kai a mansura a kasar Masar kan jami'an tsaro sinda suka kashe uku daga cikin jami'an tsaron kasar ta Masar.
Jami'an tsaron kasar Masar sun sanar da gano wasu tarin makamai a kan iyakokin kasar da kasar Libya da ake kokarin shigo da su cikin kasar.
Shafin sadarwa na jaridar Al-sharq ya bayyana cewa, kakakin rundunar sojin kasar Masar Kanar Ahmad Muhammad Ali ya sheda wa manema labarai yau a birnin Alkahira cewa, an kame makaman ne a yankin Jabal Rikham da ke yammacin kasar kuma a kan iyaka da kasar Libya, kuma yanzu haka an mika batun ga bangaren shari'a domin gudanar da bincike.
A farkon makon nan ne dai jami'an tsaron kasar ta Masar suka ce sun kame wasu manyan kwantenoni shakare da makamai da aka turo zuwa kasar ta Masar a gabar ruwa ta Alarish, kuma an turo kwantenonin ne daga kasar Turkiya, lamarin da ya kara sa jami'an tsaron kasar Masar nuna yatsan tuhuma ga kungiyar 'yan uwa musulmi da ke dasawa da gwamnatin Erdogan.
1261317
captcha