IQNA

17:38 - July 24, 2013
Lambar Labari: 2566657
Bangaren siayasa, Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa masana da masu fasaha a fagage daban-daban na rayuwa, suna da gagarumar gudunmawar da za su iya bayarwa wajen ci gaban al'ummar musulmi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da malaman jami'a da kuma marubuta gami masana adabin farisanci, inda ya ce kowane mutum yana da irin gudunmawar da zai iya bayarwa wajen ci gaban al'ummar musulmi daidai da fagensa, inda ya ce gudunmawar da malaman jami'oi za su iya bayarwa da masana adabi da kuma marubuta wajen ci gaban al'umma tana yawan gaske, idan aka yi la'akari da muhimmancin bangarensu a cikin al'umma.

Ayatollah Sayyid Ali Khamenei irin gudunmawar dam asana suka bayar wajen ci gaban al'umma a kasar Iran a bangarori daban-daban na ilimi, ya isa ya zama babban abin buga misali a duniyar musulmi, wanda kuma idan sauran al'ummomi suka bada himma za su iya yin hakan.

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa masana da masu fasaha a fagage daban-daban na rayuwa, suna da gagarumar gudunmawar da za su iya bayarwa wajen ci gaban al'ummar musulmin baki daya.

1262953

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: