IQNA

Jagoran kungiyar Hizbullah a Lebanon ya yi kira da a fito ranar Qods

17:59 - August 01, 2013
Lambar Labari: 2569634
Bangaren kas ada kasa, jagoran kungiya gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya yi kira da a fito a ranar Qods domin gudanar da gagarumin jerin gwano domin tababtar wa makiya cewa musulmi suna cikin fadaka.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jagoran kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da wani jawabi a yau bayan shan ruwa, inda zai bayyana matsayin kungiyar da kuma yadda take kallon manufar kudirin tarayyar turai a kanta. Wannan jawabi na Sayyid Nasrullah zai zo ne kwanaki biyu bayan kudirin da tarayyar turai ta amince da shi ne da ya saka kungiyar cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Jim kadan bayan fitar da wanann kudiri dai kungiyar ta Hizbullah ta fitar da wani bayani da ke cewa, kudirin tarayyar turai da ya saka ta a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda hakan ba shi da wata kima, domin kuwa kudiri ne na siyasa da haramtacciyar kasar Isra'ila ta shirya ta mika wa tarayyar turai, ita kuma ta amince da shi bisa matsin lambar Amurka. Bayanin ya ce babu wani abu wai shi bangaren soji na kungiyar Hizbullah, domin kuwa kungiyar Hizbullah kungiya daya ce mai yaki da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar musulmi.

Jawabin na Sayyid Hassanrallah shi ne na farko bayan da kungiyar tarayyar turai ta shigar da bangaren soja na kungiyar Hizbullah a karkashin sunayen kungiyoyin ta'adda. Ya kuma bayyana cewa babu wata moriya da turai za su ci daga wannan matakin da suka dauka. Dangane da cikin gida Lebanon kuwa, Sayyid Nasarallah ya kirayi masu adawa da Hizbullah da su kwana da sanin cewa ba za su iya amfani da wannan matakin ba domin cin moriyarsa a siyasance.

1266733



captcha