IQNA

Palastine na da matsayi na musammn a wajen al'ummar musulmi

17:59 - August 01, 2013
Lambar Labari: 2569636
Bangaren kasa da kasa, palastine na da matsayi na musammn a wajen al'ummar musulmi saboda haka musulmi ba za su taba mantawa da ita a cikin rayuwarsu kuma ba za su bari yahudawa su cimma burinsu an rus masallaci mai alfarma ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa daya daga cikin malaman addini a Iran ya bayyana palastine na da matsayi na musammn a wajen al'ummar musulmi saboda haka musulmi ba za su taba mantawa da ita a cikin rayuwarsu kuma ba za su bari yahudawa su cimma burinsu an rus masallaci mai alfarma bad a suke da niyyar yin hakan.

Kungiyar Hizbullah tayi a..wadai kan rushe gidajan Falastinawa da HKI keyi A bayyanan da tafitar yau laraba kungiyar ta zarki HKI da meda yankin Falastinawa gaba daya Gidajen yahudawa sannan tace shuru da kasashen larabawa na yanki suka yi tare kungiyoyin kasa da kasa ya sanya HKI na yin yanda taga dama ga Al’ummar yankin Falastinu.

Kungiyar ta nemi dukkanin kasashen larabawa da kasashen su tashi tsaye su hana wannan mummunan aiki da HKI keyi. A wannan sabon tsari da ‘yan Majalisun HKI suka tsartar Gwamnatin tasu zata kwace kasar Palastinawa dake yankin Annakab a kundancin yankin Palastinu wanda ya hada da rusa kwauyuka 36 tare rusa Gidajen Palastinawan fiye da dubu 40 Kungiyar Hizbullah ta kira wannan tsari mai hatsarin gaske.

1266673




captcha