IQNA

17:22 - August 27, 2013
Lambar Labari: 2581279

Imam Khamenei: Kasashen Da Suka Kirkiro Masu Kafirta Musulmi Ba Za Su Tsira Daga Sharrinsu Ba

Bagaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a wata ganawa da yayi a yau Litinin da sarkin kasar Oman Sultan Qabus da 'yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma, yayi ishara da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Oman inda ya ce: akwai fagage masu kyaun gaske da kasashen biyu za su iya amfani da su wajen kyautata alakar da ke tsakaninsu musamman a fagen iskar gas.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jagora cewa, Jagoran ya bayyana kasar Oman a matsayin makwabciyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hakika. Haka nan kuma yayin da yake magana kan abubuwan da suke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya, Jagoran ya bayyana cewar: a halin yanzu dai yankin nan yana cikin yanayi mai hatsarin gaske da ke bukatar aiki tare tsakanin kasashen biyu.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Babban dalilin irin wannan yanayin da yankin nan ya fada cikinsa shi ne tsoma bakin da 'yan waje suke yi cikin lamurran cikin gidan yankin.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa daya daga cikin lamurra masu tsananin hatsari da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiyan shi ne shigo da addini, bangaranci da kuma mazhaba cikin sabani na siyasa da ake da shi a wadannan kasashe yana mai cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa wasu kasashen yankin nan sun taimaka wajen kafa wata kungiya ta masu kafirta musulmi wadanda suke fada da dukkanin kungiyoyin musulmi. To amma wajibi ne masu goyon bayan wannan kungiya (mai kafirta musulmi) su san cewa wannan wutar da suka kunna su ma ba za ta barsu ba.
Har ila yau Jagoran ya bayyana haramtacciyar kasar Israila a matsayin babbar barazana ta koda yaushe ga wannan yankin wacce kuma take samun goyon bayan Amurka ido rufe, don haka sai yace: Lalatacciyar gwamnatin sahyoniyawa wacce ta mallaki rumbunan makaman kare dangi masu hatsarin gaske tana a matsayin gagarumar barazana ce ga yankin nan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: yankin nan yana bukatar tsaro na gaba daya. Ba za a iya cimma wannan manufa mai muhimmanci ba kuwa in ba ta hanyar kawo karshen makaman kare dangi a yankin nan ba.
Shi ma a nasa bangaren sarkin na Oman Sultan Qabus, wanda shugaban kasar Iran Sheik Hasan Rouhani ya ke wa jagoranci, ya bayyana farin ciki da jin dadinsa da ganawar da yayi da Jagoran juyin juya halin Musuluncin yana mai cewa alakar da ke tsakanin Iran da Oman wata alaka ce mai karfin gaske saboda alaka ta tarihi da al'adu da ke tsakanin kasashen biyu.
Sarkin na Oman ya kara da cewa: A tattaunawar da muka yi da shugaban kasar Iran mun tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi tattalin arziki musamman bangaren iskar gas. Har ila yau kuma sarkin na Oman ya jaddada abin da Jagora ya fadi na irin hatsarin da yankin Gabas ta tsakiya yake da kuma irin barazanar da haramtacciyar kasar Israila take wa kasashen yakin Gabas ta tsakiyan yana mai cewa: Fita daga irin wannan yanayi da ake ciki yana bukatar girmama maslahar al'ummomin yankin da kuma hadin gwiwa da aiki tare tsakanin kasashen yankin.
1278343
captcha