Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a wajen wannan ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana sake raya kungiyoyin ‘yan takfiriyya masu kafirta musulmi cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan a matsayin wata matsala da ma'abota girman kai suka kirkiro wa duniyar musulmi. Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da ayyukan da ‘yan wadannan kungiyoyi suke aikatawa wadanda suke taimakawa Amurka da sauran gwamnatocin ‘yan mulkin mallaka da haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawan Isra'ila wajen cimma bakaken manufofinsu musamman ma kokarin mancewa da batun Palastinu da masallacin al-Aqsa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Samar da wani yunkuri na ilimi na gama gari da yayi daidai da hankali wajen tumbuke tushen wadannan kungiyoyi masu kafirta mutane, haka nan da kuma wayar da kan mutane dangane da siyasar ma'abota girman kai na sake rayar da wannan kungiya da kuma sake rayar da lamarin Palastinu a matsayin babbar matsalar duniyar musulmi, daya ne daga cikin mafiya girman nauyin da ke wuyan malaman duniyar musulmi a wannan lokaci da muke ciki.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fara jawabin nasa ne da godiya da kuma jinjinawa Ayatullah Makarem Shirazi da kuma Ayatullah Ja'afar Subhani da sauran malaman Qum da suka ba da gagarumar himma wajen gudanar da wannan taro da kuma janyo hankulan malaman duniyar musulmi dangane da wajibcin fada da wadannan kungiyoyi masu kafirta musulmi, inda ya ce: Yayin da ake magana kan wannan kungiya ko akida mai hatsarin gaske, wajibi ne a yi la'akari da cewa babban abin da aka sa a gaba shi ne fada da wannan yunkurin da aka rayar ba wai kawai wata kungiya da ake kira Da'esh (ISIS) ba. Don kuwa a hakikanin gaske Da'esh wani reshe ne na wannan lalatacciyar bishiyar.
Daga nan kuma sai Ayatullah Khamenei ya yi ishara da wani lamari da babu kokwanto cikinsa inda ya ce: Ko shakka babu ayyukan ‘yan takfiriyya da gwamnatocin da suke goya musu baya suna biyan bukatun ma'abota girman kai, wato Amurka da gwamnatocin ‘yan mulkin mallaka na kasashen Turai da haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa. Suna nuna kansu a matsayin masu riko da Musulunci, to amma a aikace suna aiki ne wa wadancan mutanen.
Daga nan sai Jagoran yayi ishara da wasu misalai na ayyukan ‘yan takfiriyyar da suke taimakawa ma'abota girman kan cimma manufofinsu a duniyar musulmi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana gurbata yunkurin farkawa ta Musulunci da aka samu a duniyar musulmi a matsayin shaida ta farko inda ya ce: Farkawa ta Musulunci da aka samu wani yunkuri ne na fada da Amurka, mulkin kama-karya da ‘yan amshin shatan Amurka. To amma ‘yan takfiriyya sun mai da wannan gagarumin yunkuri na fada da girman kan zuwa ga wani yaki na basasa da zubar da jinin juna tsakanin musulmi.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: "Isra'ila" ita ce fili dagan ‘yan gwagwarmaya musulmi a wannan yankin, to amma ‘yan takfiriyya sun sauya wannan fagen dagan, inda suka mayar da shi kan titunan kasashen Iraki, Siriya, Pakistan da Libiya. Wannan kuwa daya ne daga cikin manyan laifuffukan ‘yan takfiriyyan da ba za a taba mantawa da su ba.
Jagoran ya bayyana gurbata wannan yunkuri na farkawa ta Musulunci (da ‘yan takfiriyyan suka yi) a matsayin babbar hidima ga Amurka da Ingila da haramtacciyar kasar Isra'ila da kungiyoyin leken asirinsu, yana mai cewa: Wata shaidar kuma da take nuni da cewa ayyukan ‘yan takfiriyyan suna biyan bukatun ma'abota girman kai, ita ce cewa masu goyon bayan ‘yan takfiriyyan ba sa taba daga kara wajen fada da haramtacciyar kasar Isra'ila, kai face ma dai suna hada kai da ita ne wajen yakar musulmi. Amma su ne a sahun gaba wajen cutar da kasashe da al'ummomin musulmi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana rusa tushen ababe masu kima da tsarki na kasahen musulmi da ‘yan takfiriyyar suke yi a matsayin wani misali na daban na irin ayyukan da suke aikatawa wajen biyan bukatun makiya Musulunci, inda ya ce: Wani aikin na daban mai munin gaske da ‘yan takfiriyyan suke aikatawa shi ne shafa wa wannan addini mai cike da rahama da hikima na Musulunci kashin kaji ta hanyar nuna wasu hotuna masu muni irin su sare kawukan mutanen da ba su ci ba su sha ba, ko kuma ciro zuciyar wani musulmi da tauna ta a gaban kyamarori sannan kuma da sunan Musulunci.
Wani misalin kuma da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kawo da ke tabbatar da irin hidimar da masu akidar takfiriyya suke yi wa manufofin ma'abota girman kan duniya shi ne irin yadda suka fita sha'anin dakarun gwagwarmaya a yakin kwanaki 50 a Zirin Gaza. Daga nan sai Jagoran ya ce: Wani misalin kuma shi ne yadda suka kautar da kumajin da matasa musulmi suka samu albarkacin wannan farkawa ta Musulunci da kuma amfani da hakan wajen kashe musulmin da ba su ci ba su sha ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin yadda jiragen daukan kaya na Amurka suke watsa wa ‘yan kungiyar Da'esh makamai da sauran kayayyakin soji ta sama a kasar Iraki a matsayin wani misali na daban, inda ya ce: Duk da irin wadannan abubuwa, amma Amurka a zahiri tana ikirarin kafa hadakar fada da kungiyar Da'esh, wanda hakan karya ce tsagoronta. Don kuwa asalin manufar wannan hadakar ita ce tabbatar da wannan fitina ta yaki da zubar da jini tsakanin musulmi. Duk kuwa da cewa ba za su cimma wannan manufa ta su ba.
Daga nan kuma sai Ayatullah Khamenei yayi ishara da gagarumin nauyin da ke wuyan malaman duniyar musulmi a irin wannan yanayi da ake ciki yana mai cewa: Daya daga cikin wadannan nauyin shi ne samar da wani yunkuri na gama gari na ilimi da hikima da malaman mazhabobin Musulunci za su yi wajen tumbuke tushen wannan kungiyar.
Jagoran ya ci gaba da cewa: ‘Yan wannan kungiyar sun shigo fage ne da taken karya na riko da salihan magabata. Don haka wajibi ne a yi amfani da karantarwa ta addini da ilimi wajen nuna wa duniya cewa salihan magabatan ba su yarda da wannan aikin ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wajibi ne a yi amfani da ilimi da hikima wajen ceto matasan da ba su ci ba su sha ba wadanda suka fada tarkon wannan bakar akida. Wannan kuwa wani nauyi ne da ke wuyan malamai.
Ayatullah Khamenei ya bayyana wayar da kan al'umma dangane da rawar da siyasar Amurka da Ingila da haramtacciyar kasar Isra'ila suka taka wajen sake dawo da wannan mummunar akida ta takfiriyya a matsayin wani aiki mai girma da ke wuyan malaman addini na kasashen musulmin, daga nan sai ya ce: nauyi na uku da ke wuyan malaman, shi ne ba da muhimmanci na hakika ga matsalar Palastinu da masallacin Al-Aqsa da kuma shiga gaban duk wani abin da zai sanya musulmi mantawa da wannan lamarin.
Yayin da yake ishara da matsaya ta baya-bayan nan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka na sanar da kasar Palastinu a matsayin kasar yahudawa, Jagoran ya ce: Babban abin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta sa a gaba shi ne kwace Kudus da masallacin Al-Aqsa da kuma raunana Palastinawa. Wajibi ne dukkanin al'ummar musulmi, haka nan kuma da malaman Musulunci su bukaci gwamnatocinsu da su tsaya kyam wajen neman tabbatar da hakkokin Palastinawa.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan matsayar marigayi Imam Khumaini, yardar Allah ta tabbata a gare shi, ta goyon bayan Palastinu da kuma kiyayya da haramtacciyar kasar Isra'ila, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Muna gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya hada bakunan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, gwamnati da al'ummar kasar wajen goyon bayan Palastinawa da kuma kiyayya da haramtacciyar kasar Isra'ila, sannan kuwa tsawon shekaru 35 din da suka gabata ba su kauce daga wannan tafarki da marigayi Imam ya tsara ba.
Yayin da yake magana kan yadda matasan Iran suke ci gaba da riko da wannan tafarki na taimakon al'ummar Palastinu da kuma shaukin da suke da shi na yin fito na fito da sahyoniyawa ‘yan share guri zauna, Ayatullah Khamenei ya ce: Cikin yardar Allah da tausayawarsa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta fada tarkon sabani na mazhaba ba. Kamar yadda take taimakon kungiyar ‘yan Shi'a ta Hizbullah a kasar Labanon, haka nan take taimakon kungiyar Hamas da Jihadi Islami da sauran kungiyoyi na Ahlussunna a Palastinu. Kuma za ta ci gaba da wannan taimakon.
Jagoran ya bayyana irin karfin da Palastinawa suka yi a Gaza a matsayin daya daga cikin misalan irin taimakon Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al'ummar Palastinu don haka sai ya ce: Kamar yadda a baya na fadi, wajibi ne a karfafa Yammacin kogin Jordan da makami don kare kansu. Ko shakka babu za a yi hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar a halin yanzu dai makiya duniyar Musulunci sun yi rauni ainun sama da shekarun da suka gabata yana mai ishara da irin matsaloli na siyasa da tattalin arziki da tsaro da kasashen Turai hakan da kuma tsaka mai wuyan da Amurka take ciki a fagen siyasa da tattalin arziki. Daga nan sai Jagoran ya ce: Haramtacciyar kasar Isra'ila ma dai ta yi laushi da rauni ainun idan aka kwatanta ta da shekarun baya. Wannan gwamnatin, ita ce dai gwamnatin da a baya take yawo da taken za ta mamaye daga Nilu zuwa Furat. To amma a halin yanzu a lokacin yakin kwanaki 50 a Gaza, ta yi amfani da dukkanin karfin da take da shi, amma ta gagara ruguza ramukan karkashin kasa da dakarun Hamas da Jihad suke amfani da su.
Har ila yau Ayatullah Khamenei ya yi ishara da irin matsaloli da kashin da makiya Musulunci suka sha a yankin Gabas ta tsakiya musamman a kasashen Iraki da Siriya da Labanon, daga nan sai ya ce: Wani misali na raunin makiya, shi ne kan shirin nukiliyan kasar Iran. Amurka da kasashen ‘yan mulkin mallaka na Turai sun hadu waje guda don su dunkufar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da wannan shiri nata na nukiliya, amma sun gaza. A nan gaba ma ba za su iya ba.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da Hujjatul Islam wal muslimin Alizadeh Musawi, sakataren "Taron Kasa Da Kasa Kan Kungiyoyin Takfiriyya A Mahangar Malaman Musulunci" ya gabatar da rahotonsa kan yadda aka gudanar da taron da kuma abubuwan da aka cimma inda ya ce: A yayin taron dai an kafa kwamitoci guda hudu wadanda suka tattauna kan batutuwa guda hudu ya ba su muhimmanci su ne: Tushen ‘yan Takfiriyya da kungiyoyi masu tsaurin ra'ayi; dubi cikin tushen da akidar takfiriyya ta ginu a kai; alala tsakanin siyasa da ‘yan takfiriyya sai kuma hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen akidar takfiriyya da hanyoyin da za a bi wajen fada da su.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da tarurrukan share fagen da aka gudanar kafin wannan taron a kasashen Siriya da Pakistan, da kuma makaloli sama da 700 da aka tattaro, Sheikh Alizadeh Musawi ya ce: Malamai da masanan kasashen musulmi su 315 ne suka halarci taron. Har ila yau kuma an buga da kuma yada zababbun makaloli 144 cikin mujalladai takwas da aka fassara su zuwa harsunan Farisanci da larabci.
2611603