sadarwa na yanar gizo na cath.ch cewa a jiya ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan wurin bautar kildaniyawa agarin Mausil na kasar Iraki, inda ruka rusa wurin mai tsawon tarihi suka nike shi baki daya.
Daya daga cikin shugabannin kabilun larabawa 'yan sunna a garin Mausil wa wata tashar talabijin a daren jiya cewa, baya ga rusa wannan wuri ma 'yan ta'addan na ISIL sun kashe wani malami a birnin bayan da suka bukaci da ya mika musu masallacin annabi yunus amincin Allah ya tababta a gare shi, kuma ya bayar da fatawar haramcin barin kiristoci a cikin garin na Mausil, inda ya sheda musu cewa ba zai yi hakan ba, a nan take suka yanka shi.
A nasu bangaren sojojin kasar Iraki suna ci gaba da nausawa a cikin yankunan da 'yan ta'addan suka kwace iko da su, inda suke ci gaba da fatattakarsu, domin dawo da doka da oda a yankunan, da kuma dawo da dubban daruruwan mutanen da 'yan ta'addan suka kora daga yankunansu.
2612268