IQNA

Malaman Cibiyar Azhar Sun Gargadi Dangane Da Yin Afmani Da Kur'ani Don Manufar Siyasa

23:03 - November 27, 2014
Lambar Labari: 2612424
Bangaren kasa da kasa, manyan malaman babbar cibiyar muslunci a kasar Masar ta Azahar sun yi gargadi dangane da yadda wasu suke yin amfani da kur'ani domin cimma buri na siyasa akasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-youm Sabi cewa masana da shugabanni a babbar cibiyar muslunci a kasar Masar ta Azahar sun yi gargadi dangane da yadda wasu suke yin amfani da kur'ani domin cimma buri na siyasa tare da bayyana hakan da cewa ya sabawa koyarwar wannan addini.

Matakin dai ya zo ne sakamakon abin da wasu daga cikin magoya bayan kungiyar yan musulmi suke yi ne a lokacin da suke yin a jerin gwano da gangami a kasar sukan daga kur’ani, wanda kuma hakan ya tabbata a tarihin muslunci cewa wadanda suka fara yin wannan abu mayaudara ne kuma sun rudi wasu wawaye daga cikin muslumi, wanda hakan ya zama babban abin da ya kawo rarraba tsakanin musulmi a lokacion da ake kokarin murkushe wadanda suke kokarin bata sunan wannan addini mai tsarki.

Bayanin ya ya ci gaba da cewa wasu yan siyasa sun mayar da sauran mutane musulmi tamkar wawaye, domin kuwa a lokacin da mutum ke bukatar bayyana matsayinsa babu bukatar ya yi yaudara da kur’ani, domin kuwa dukkanin maganar da ake yi ta siyasa ce da neman mulki da matsayi, ko da mutum ya yi amfani da sunan addini wajen kamfe, to bai dace kuma kur’ani ya zama a bin wasa da yaudara ta siyasa ba kamar dai yadda ake gani a kasar.

Wasu daga cikin malamai da masana  a kasar dai suna sukar irin wannan mataki da mabiya kungiyar yan uwa musulmi suke dauka na yin amfani da kur’ani mai tsarki tare da daga  shi a gaban jami’an tsaron Masar a lokacin zanga-zanga, wanda hakan kan kai ga tozarta matsayin wannan babban littafi mai tsarki.

2612300

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha