Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jagora cewa, lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wannan ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana jin nauyi na dan'adamtaka da kuma nauyi na Ubangiji da kuma basira a matsayin tushe na asali na tunani da hikimar Basiji. Haka nan kuma yayin da yake jinjinawa kokari da tsayin dakan tawagar Iran a wajen tattaunawar nukiliya da manyan kasashen duniya, Jagoran ya bayyana cewa al'ummar Iran ba sa bukatar neman yardar Amurka cikin wannan tattaunawar inda ya ce: A saboda haka ne ban nuna adawa ta ga asalin tattaunawar ba, haka nan ma da sake sabonta wa'adin tattaunawar, kuma za mu amince da duk wata matsaya ta adalci sannan kuma wacce ta yi daidai da hankali da aka cimma. To amma mun san cewa ita wannan gwamnatin ta Amurka ita ce take bukatar cimma yarjejeniyar. Sannan kuma ita ce za ta cutu daga duk wani rashin cimma yarjejeniya, don kuwa idan ma daga karshe ba a kulla yarjejeniyar ba, to Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta cutu ba. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hada tunani da ilimi da hikima tare da kumaji da so da kauna da take tare da mutum a matsayin sirrin nasarorin da dakarun Basijin suka samu a fagage daban-daban inda ya ce: Tushe na asali na tunanin Basiji wanda kuma aka samo shi daga tushe na addini, shi ne jin nauyi na dan'adamtaka da kuma na Ubangiji dangane da shi kansa mutum din iyalinsa da kuma al'umma baki daya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Tushe na biyu na tunanin Basiji wanda mai kammala na farko ne sannan kuma sharadinsa na lazimi shi ne basira da kuma fahimtar zamanin da ake ciki da kuma bukatar da ake da shi; haka nan da fahimtar aboki da makiyi da kuma hanyoyin fada da shi. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana rashin basira a matsayin share fagen fadawa cikin shubuha da rashin fahimta ko kuma gurbatacciyar fahimta, don haka sai ya ce: Mutanen da ba sa da basira, tamkar wadannan miskinan da suka fada tarko ne a lokacin fitinar shekara ta 2009 ne wadanda suke gudanar da ayyukansu cikin wannan yanayi da ke cike da kura. A irin wannan yanayin ne suka zamanto masu taimaka wa makiya da kuma cutar da masoyi. Haka nan kuma yayin da yake maganan kan cewa jin nauyi ba tare da basira ba wani lamari ne mai hatsarin gaske, Ayatullah Khamenei ya ce: Akwai wasu mutane a lokacin gwagwarmaya kafin nasarar juyin juya halin Musulunci, cikin shekaru talatin din da suka gabata da suka zamanto masu jin nauyi a wuyansu amma ba tare da basira ba, don haka suka dinga aikata wasu abubuwa da suka cutar da wannan yunkuri na marigayi Imam, juyin juya halin Musulunci da kuma kasar (Iran). Sannan kuma yayin da yake sake jaddada tunatarwar da ya dinga yi a lokacin fitinar shekara ta 2009 dangane da batun amfani da basira, Jagoran cewa ya yi: A wadancan ranakun wasu suna nuna fushinsu dangane da maimaita batun basira da ake yi, to amma a halin yanzu ma ina sake jaddada wajibcin basirar. Don kuwa hatsarin da ke cikin kumaji ba tare da basira ba, ya fi yawa. Babu wani tabbaci da ake da shi kan wannan mutumin. Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin matakan da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya dauka na yin bayanin abubuwan da suka dinga faruwa da kuma matakan da ya kamata a dauka kansu, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Imam Khumaini (r.a) ne ya ba da umurnin kafa cibiyar Basiji da kuma tsara manufar kafa ta inda ya ce: "Duk wani Allah wadai da kuke da shi, ku yi shi a kan Amurka". Har ila yau yayin da yake ishara da sanannen maganar nan ta marigayi Imam Khumaini (r.a) da ke cewa: "Kiyaye wannan tsarin, shi ne mafi girman wajibai", Jagoran cewa ya yi: Mutanen da ba su fahimci jawaban Imam (r.a) ba, a wasu lokuta su kan tabka gagaruman kura-kurai. A saboda haka sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Ko da wasa bai kamata a gafala daga batun jin nauyi a matsayin tushen tunanin Basiji sannan basira kuma a matsayin sharadi na wajbi. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce da irin wannan mahangar ce za a iya fassara ma'anar Basiji inda ya ce: Duk wani mutum da yake jin akwai wani nauyi a wuyansa sannan kuma ya ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya dace, a ko ina yake, shi dan Basiji ne. A saboda haka mafi yawa sosai na al'ummar Iran, ‘yan Basiji ne. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da ayyuka daban-daban da dakarun sa kai na Basijin suka gudanar tsawon shekarun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran a fagagen ilimi daban-daban, don haka daga karshe sai ya ce: Irin wannan tunani na Basiji wanda marigayi Imam Khumaini (r.a) ne ya samar da shi, a halin yanzu dai ya watsu zuwa wajen Iran tamkar wata iska mai kadawa ce da babu wanda ya isa ya dakatar da ita. Ayatullah Khamenei ya ce: A halin yanzu ana iya ganin wannan tunani na Basiji a kasashen Iraki, Siriya, Labanon da kuma Gaza. Insha Allahu nan ba da jimawa ba, sai an gan shi a Kudus mai tsarki don ‘yanto Masallacin Al-Aqsa mai alfarma. Don hake ne Jagoran ya ce: Albarkacin wannan tunani ne ya sanya ba za a iya yin galaba a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Asalin mahangar tsarin Musulunci (na Iran) shi ne fada da girman kai da gwamnatin girman kai ta Amurka. Don haka bai kamata a yi rauni ko sanyi ko kuma a yi kure kan wannan tafarkin ba. Tabbas mu dai ba mu da matsala da mutane ko kuma kasar Amurka, face dai matsalarmu da girman kai da tinkaho da karfi na gwamnatin Amurkan ne. Yayin da ya koma kan batun tattaunawar nukiliya da Iran take yi da manyan kasashen duniya da kuma sake sabunta wa'adin tattaunawar, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Saboda wannan dalilin ne ya sanya ban yi adawa da asalin tattaunawar ba, haka nan ma da sake sabunta wa'adinta. To amma wajibi ne a yi la'akari da wasu batutuwa. Jagoran ya bayyana tawagar Iran a wajen tattaunawar da mutane masu kokari ba kama hannun yaro kana kuma masu kishin kasa da kuma gudanar da ayyukansu cikin hikima inda ya ce: A hakikanin gaskiya tawagar Iran sun tsaya kyam a gaban girman kan masu tinkaho da karfi, sabanin daya bangaren. Yayin da yake magana kan irin harshen damo da Amurkawa suke yi cikin maganganu da ayyukansu, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: A maganganunsu na bayan fage da kuma wasikun da suke aikowa, suna fadin wani abu daban, a jawaban na jama'a kuma wani abin na daban suke fadi. Haka nan kuma yayin da yake ishara da matsaloli daban-daban na ‘diplomasiyya, siyasa da kafafen watsa labarai da Iran ta fuskanta a yayin wannan tattaunawar, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Wadannan mutanen sun fito da maitarsu a kan masu tattaunawarmu, sannan kuma a cikinsu Amurka ta yi mummunan hali ita kuma Ingila ta fi cutarwa. Imam Khamenei ya ci gaba da cewa: Ya kamata al'ummar Iran da kuma tawagar masu tattaunawar su san cewa koda ma dai tattaunawar ba ta kai ga natija ba, Amurka ita ce za ta fi cutuwa, ba mu ba. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Na yi amanna da cewa hakikanin manufar ma'abota girman kan ita ce hana ci gaba da kuma daukakar da al'ummar Iran suke samu. Jagoran ya bayyana batun nukiliya a matsayin wani batu kawai da ma'abota girman kan suke fakuwa da shi, inda ya ce: Koda yake suna da wasu abubuwan da suke fakewa da su din, to amma manufarsu ta hakika ta takunkumin da suka sanya wa Iran ita ce dakatar da ci gaban kasar Iran. Haka nan kuma yayin da yake ishara da abubuwan da kafafen watsa labaran kasashen yammaci suke fadi dangane da raguwar irin kaunar da Amurka suke yi wa shugaban Amurkan na yanzu a matsayin da ke nuni da irin sabanin da ke tsakanin jami'an Amurka da al'ummar kasar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin gagarumar bukatar da Amurka take da ita ga wannan tattaunawar da ake yi inda ya ce: Saboda irin wadannan matsalolin da suke ciki ne ya sanya jami'an Amurka suke tsakanin bukatar wata nasara da za su nuna. Jagoran ya ce: Amma sabanin Amurkan, mu dai ko da ba a kai ga gaci ba yayin tattaunawar, babu wata matsala da za mu fuskanta. Don kuwa muna da hanyar da muka tsara mai suna tsarin tattalin arziki na gwagwarmaya. Har ila yau kuma yayin da yake ishara da maganganun wasu jami'an Amurkan bayan sabunta wa'adin tattaunawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Suna fadin cewa wajibi ne Iran ta kwantar wa kasashen duniya hankali. To akwai dai wasu abubuwa guda biyu na kuskure cikin wannan maganar. Jagoran ya ce: Batu na farko shi ne cewa ‘yan wadannan kasashen, sun sa wa kansu sunan kasashen duniya. Da wannan magana ta su, sun yi watsi da kimanin kasashen 150 na kasashen kungiyar ‘yan ba ruwanmu da kuma biliyoyin mutanensu da mai she su ba a bakin komai ba. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Batu na biyu shi ne cewa mu dai ba ma bukatar yarda ko kwantar wa Amurka da hankali, kuma ba ma son hakan. Don kuwa ba shi da wani muhimmanci a gare mu. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Su din nan ma'abota girman kai ne, mu kuwa ba ma zama inuwa guda da ma'abota girman kai. A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da maganganun jami'an Amurka dangane da wajibcin kiyaye tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila a yayin wannan tattaunawar inda ya ce: Ya kamata ku san cewa ko an cimma yarjejeniyar nukiliya ko ba a cimma ba, a kullum Isra'ila za ta ci gaba da zama cikin rashin aminci da kwanciyar hankali. Jagoran ya ce hatta cikin wannan magana ma jami'an Amurkan ba su da gaskiya don kuwa babban abin da suka sa a gaba shi ne lamunce manufofinsu na daidaiku, ba wai tsaron Isra'ila ba. Jagoran ya ci gaba da cewa: Babbar manufar jami'an Amurka, ita ce kwantar wa ‘yan jari hujjan sahyoniyawa na duniya, don kuwa suna ba su rashawa da kudade. Idan kuwa ba su yi hakan ba, to suna iya musu barazana kai har ma da kisa. Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci sai da babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari da kuma Manjo Janar Muhammad Ridha Naqdi, shugaban cibiyar Basij din na Iran suka gabatar da jawabansu dangane da ayyukan da Basij din suka gudanar da kuma irin tsare-tsaren da ake da su wajen ci gaba da karfafa dakarun na Basij. 2612390