IQNA

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon Ya Yi Allawadai Da Harin Najeriya

21:40 - November 30, 2014
Lambar Labari: 2613511
Bangaren kasa da kasa, sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban-ki-moon yayi allawadai da kuma bukatar a hukunta duk wani mai hannu a hare-haren kunar bakin wake da suka salwantar da rayukan fiye da mutane da dama a babban masalacin jihar Kano dake Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Times cewa, Ban Ki-moon ya kuma yi tir da abin da ya faru a Kano, yana mai kira ga hukumomin wannan kasa da su dauki matakan gano wadanda suka yi wannan aika-aika, tare da gurfanar da su gaban kuliya.  
Shugaban wanan kasa ya nuna takaici sossai da wanan harin, yana mai lasar takobin cewa wadanda keda hanu a wanan ta'adi sai sunyi nadamar aikata wanan aiki. Shi kwa Mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu wanda ya katse aikin Umrah da ya ke yi a Saudiyya, saboda harin da a ka kai ya shawarci al'umma da kadda abunda ya faru ya basu tsoro riko da addini.  
Harin dai da aka kai a babban masalacin na Kano ran juma'a data wuce an tabbatar  cewa yayi sanadin mutuwar mutane akalla dari da ashrin yayin da wasu karin dari biyu da sabain suka sami munanan raunuka, wadanda yanzu haka ake ci gaba da kula da wasu a wasu asibito da ke cikin birnin na kano,
Wannan lamari dai shi ne irinsa na farko da aka taba  gani a birnin na kanno inda aka kai hari kan masallata a masallacin juma a ranar juma’a tare da kshe mutane masu tarin yawa, tuni dai jami’an tsaro suka shiga gudanar da bincike kan wannan lamari.
  
2612987

Abubuwan Da Ya Shafa: Moon
captcha