IQNA

Darul-Ifta A Masar Ya Ce Daesh Suna Kashe Mata Da Sunan Muslunci

22:58 - December 11, 2014
Lambar Labari: 2617672
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar ta bayyana kungiyar yan ta'addan daesh da cewa tana tafka barna da kashe mata da kanan yara duk da sunan yaki a addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na Al-wafd cewa, Darul Ifta wadda it ace babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar ta bayyana kungiyar yan ta'addan daesh da cewa tana tafka barna da kashe mata da kanan yara duk da sunan yaki a addini wanda hakan yake bakanta sunan wannan addini mai darja a idon duniya.

Babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Masar Sheikh Shauqi Al-allam ya bayyana cewa kungiyar da ake kira Daular Musulunci a Iraki da Sham (ISIS) gungu ne na 'yan ta'adda tantagarya.  
A cikin wani bayani da ofishin da ke a cibiyar Darul Ifta a birnin Alkahira ya fitar a jiya Talata, ya ce 'yan ta'addan kungiyar ISIS bai halasta ba a shar'ance a danganta su da addinin musulunci, domin dukkanin abin da suke yin a ta'addanci da sunan jihadi a cikin kasashen Syria da Iraki ya yi hannun riga da addinin muslunci da kuma koyarwar sunna irin ta manzon Allah.
Shehin malamin ya yi Allawadai da rusa kabrukan annabawa da salihan bayi gami da masallatai da majami'oi da 'yan kungiyar ta ISIS suke yi yanzu ahak a cikin kasashen Syria da Iraki, tare da muzantawa da kuma cin zarafin marassa rinjaye da suka mamaye yankunansu, musamman kiristoci da kuma Izidawa da kuma sauran bangarori na musulmi da dukkanin bangarorinsu.
2617351

Abubuwan Da Ya Shafa: Darul Ifta
captcha