Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, a ci gaba da cin zarafin malaman addinin muslnci mahkuntan kasar Bahrain sun sake yin barazana a kan wani babban malamin Sheikh Ali Bin Ahmad Aljid Alhafsi daya daga cikin fitattun malamai na kasar.
A cikin rahotonta kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya ta zargi gwamnatin Bahrain da azabtar da kananan yaran da ta ke tsaro da su, a wani bayani da kungiyar ta fitar ta ambaci cewa a tun daga dubu biyu das ha daya ne ake azabtar da kananan yara masu yawa da ake tsare da su ta hanyar duk.
Rahoton ya ci gaba da cewa wasu daga cikin yaran sun fuskanci barazanar yi musu fyade domin tilasta su yin furuci. Mataimakin Shugaban Kungiyar a gabas ta tsakiya da kuma arewacin Maduha ya ce; Kame da tsare kananan yara da gwamnatin Bahrain ta ke yi, yana nuni ne da yadda ta ke take hakkokin bil’adama.
Jami’in ya kira yi gwamnatin Bahrain da ta saki dukkanin yaran da shekarunsu su ke kasa da 18 wanda babu wani laifi da su ka aikata, tare da kuma da gudanar da bincike akan take hakkin bil’adama.” Rahoton kungiyar ya ce; Da akwai yaran da adadinsu ya kai dari das ha daya da ake tsare da su wadanda kuma shekarunsu su ke a tsakanin sha shida zuwa sha takwas.
2617372