Kamfanin dillancin labarai na Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na OnIslam cewa, shugaban majalisar musulman kasar ta Kenya bdulgafur yana fadar haka ya kuma kara da cewa dole ne gwamnatin kasar ta bode masallatan da ta rufe a birnin da sunan yaki da ta’addanci.
Ministan ya kara da cewa abinda gwamnatin kasar Kenya take yi da musulman kasar Kenya yana dai dai da cewa dukkan musulman kasar Kenya dan ta’adda ne.
Labarin ya kara da cewa a makon da ya gabata kadai yan sanda masu yaki da ta’addanci a kasar sun kai farmaki kan masallatai da dama a birnin Mombasa suka kama matasa da dama suka kuma rufe masallatan.
Majalisar musulman tana ganin jami’an tsaron kasar su na wuce gona da iri wajen yaki da yan ta’addanci ta yadda abin yakan shafi wadanda basu san hawa ko sauka ba daga muuslmi.
A cikin 'yan kawanakin dai an samu kai hare-hare a cikin kasar anda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, wanda kuma kungiyar yan ta'addan da ke da alaka da sauran 'yan ta'adda na kasa da kasa ta dauki nauyin hakan.
2617531