IQNA

An Gudanar Da Jerin Gwanon Ranar Duniya Na Kin Amincewa Da Kyamar Muslunci

17:47 - December 14, 2014
Lambar Labari: 2618354
Bangaren kasa da aksa, an gudanar da gagarumin jerin gwano a ranar 13 ga December a birnin Paris domin nuna rashin amincewa da yadda kungiyoyin masu kamar adinin muslunci a kasar suke ta kara zafafa adawarsu ga musulmi duk kuwa da cewakafofin yada labarai sun yi kan hakan.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ajib cewa, a cikin wannan makon an gudanar da gagarumin jerin gwano a biranan turai da dama da suka hada da Amstardam, London, da kuma Brussel.
Bayanin ya ci gaba da cewa birnin pari an gudanar da ita cea  cikin haramin jami’ar babban birnin kasar domin nuna rashin amincewa da yadda kungiyoyin masu kamar adinin muslunci a kasar da ma wasu kasashen yammacin turai suke ta kara adawarsu ta kin musulmi da kuma addininsu.
Wannan dai bas hi ne karon farko da ake gudnar da irin wannan jerin gwanoa  cikin wadannan kasahse ba, domin kuwa an jima ana samun matsaloli makamantan hakan, amma kuma musulmi suna yin hakuri, duk kwa da cewa akwai wadanda ba musulmi ba da suke nuna musu kara wajen jerin gwanon.
2618086

Abubuwan Da Ya Shafa: Islamophobia
captcha