Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Oumma cewa, an fitar da film din mai suna (Nacido en Gaza) wanda ke magana kan yakin da yahudawa suka kaddamar kan al'ummar wannan yankin a cikin shkra ta 2014, da kuma yadda rayuwar wasu yara 10 kana ta kasance.
Bayan watanni uku da kawo karshen yakin da Isra'ila ta kaddamar a yankin an harhada abubuwa da dama da suke da alaka da yakin, da kuma irin rashin imanin da yahudawan suka nuna, lamarin day a yi sanadiyyar mutuwa tare da jikkatar dubban mutanen, da suka hada da mata da kuma kananan yara, tare da rushe wuraren ibada da suka hada da masallatai da sauransu.
Wannan yaki dai ya lashe rayukan mutane 2140 daga suka hada da kananan yara 507, haka nan kuma wasu 10 daga cikinsu na daga cikin wadanda labarinsu ya zagaye duniya, sakamakon halin da suka samu kansu a ciki na rashin imani daga yahudawan sahyuniya, inda ake bayyana abin day a faru nay akin Gaza da cewa tun shekarar da aka yi yakin duniya, inda aka yi wa fararen hula kisan kiyashi.