IQNA

Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ga Kwamandoji Masu Atisayi

19:03 - December 29, 2014
Lambar Labari: 2649121
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gana da wasu daga cikin kwamandoji da jami'an dakarun sojin ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a jawabin da ya gabatar yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ruhin gwagwarmaya da tsayin daka a matsayin abin da ke kare mutumci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Jagoran juyin juya halin muslunci cewa Jagoran juyin juya halin Musuluncin wanda kuma shi ne babban kwamandan sojin Iran ya bayyana karfafa azama da shirin sadaukarwa a matsayin wani lamari da ya zama wajbi, daga nan sai ya ce: Darasin da Alkur'ani mai girma ya koya mana shi ne cewa, ana iya yin nasara a kan makiyi koda da ‘yan wasu makamai ne matukar dai aka sami imani mai karfi da kuma ruhin tsayin daka.
Haka nan kuma yayin da yake dangane da tekunan da suke kewaye da Iran da kuma irin kudaden da makiya suke kashewa a yankin Tekun Fasha da nufin cimma manufofinsu, Jagoran cewa ya yi: Wajibi ne dakarun sojin ruwanmu so kara irin shirin da suke da shi ba tare da la'akari da wasu lissafe-lissafe na siyasa ba. Kamar yadda kuma wajibi ne su san gibin da suke da shi da kuma raunin da makiyi yake da shi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana lokacin sulhu da zaman lafiya a matsayin wani lokacin da ya kamata a yi amfani da shi wajen fadada fagen ilimi, gina kasa da kuma kara karfi na kariya.
A karshen jawabin nasa, babban kwamandan dakarun soji na Iran din, ya yi ishara da irin sadaukarwar da dakarun sojin ruwan na Iran suka yi a fagage daban-daban musamman a lokacin kallafaffen yaki (na shekaru takwas da tsohuwar gwamnatin Iraki ta tilasta wa Iran) inda ya ce: A koda yaushe dakarun sojin ruwan sun zamanto wata alama ta tabbatar da mutumci da kuma matsayin sauran dakarun soji da kuma kasar nan baki daya. Don haka tarihi da kuma sadaukarwa shahidan dakarun sojin ruwa, ciki kuwa har da shahidan jirgin ruwan Peykan za su ci gaba da zama cikin tarihin wannan kasa ta mu.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da Rear Admiral Sayyari, kwamandan dakarun sojin ruwan na Iran ya gabatar da jawabinsa, inda yayin da yake magana kan tunawa da ranar 7 ga watan Azar (ranar sojin ruwa na Iran) yayi karin haske kan wasu daga cikin ayyukan da rundunar sojin ruwa take gudanarwa da nufin karfafa irin karfin da take da shi wajen kare kasar Iran daga duk wata barazana daga makiya.
2648069

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha