
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, bisa ruwaya ta Ahlu Sunnah, ranar 12 ga wata Rabi’ul Awwal shi ne ranar haihuwar manzo, wanda bisa hakan a jiya Laraba mabiya addinin muslunci a birnin Prophit na kasar Faransa sun gudanar da taron maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa kamar dai yadda aka saba gudanarwa a wasu biranan kasar.
Kasar Faransa dai na daga cikin kasashe da ke yawan musulmi kasantuwar kasar tana da alaka da kasashen larabawa da ta yi wa mulkin mallaka musamman daga kassahen larabawan yankin arewacin nahiyar Afirka, wadanda wasu daga cikinsu suna zaune a kasar ta Faransa, yayin da wasu kuma ske da alaka da kasar ta wasu hanyoyi.
Gudanar da tarukan maulidin manzon Allah a wannan birnin a wannan karo wata manuniya ce dangane da irin ci gaban da musulmi suke samu a kasar, da kuma yadda wannan addini yake ci gaba da kara yuwaduwa da bazuwa wasu yankuna na kasar.
2667290