IQNA

Azhar Da Majami’ar Kibdawa Sun Yi Allah Wadai Da Ziyarar Shugaban OIC a Quds

23:18 - January 06, 2015
Lambar Labari: 2679861
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar muslunci ta Azhar da kuma babbar majami’ar kasar sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da ziyarar shugaban kungiyar OIC a birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nan a jaridar Almisriyun cewa, a jiya cibiyar muslunci ta Azhar da kuma babbar majami’ar kasar Masar duk sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da ziyarar shugaban kungiyar kasashen musulmi taOIC a birnin Quds karkashin kulawar yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban kungiyar ta OIC ya kai wanann ziyara ne domin ganewa idanunsa abin da yake faruwa  abirnin, amma da dama daga cikin kasashen larabawa suna ganin bai kamata ba, domin ko ba komai ya zai yi amfani da takardun shiga ne da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta bas hi, wanda hakan yana nuna wani bangare ne na amincewa da halscin gwamnatin yahudawan.
Shugaban kungiyar ta daio ya bayyana wannan ziyara tasa da cewa bai yi ta domin muzgunawa wani bangare na muuslmi ba, bil hasali ma ya yi hakan ne domin duba halin da palastinawa suke ciki ne a birnin Quds mai alfarma, domin sanin hanyoyin da ya kamata a bi domin taimakonsu.
Yanzu haka dai an bukace da ya yanke ziyarar tare da komawa gida ba tare da wani bata lokaci ba, domin kada haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da hakan wajen tabbatar da halascinta a yankin gabas ta tsakiya.
2677804

Abubuwan Da Ya Shafa: Palestinu
captcha