IQNA

Kawo Rarraba Tsakanin Al’umma Ya Saba Wa Abin Da Al’umma Take Bukata

10:12 - January 08, 2015
Lambar Labari: 2684351
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran a lokacin da yake ganawa da dubban mutanen birnin Qom ya bayyana cewa, kawo rarraba tsakanin al’umma da kowane suna ya yi hannun riga da abin da al’ummar take bukata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, a safiyar Laraba 7-1-2015 ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan mutanen birnin Qum da suka kai masa ziyara don tunawa da zagayowar ranar yunkurin 19 ga watan Dey na al’ummar birnin na Qum.
A jawabinsa yayin wannan ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da wajibcin fada da kokarin makiya na jirkita hakikanin koyarwar juyin juya halin Musulunci na Iran da kuma kokarin sanya a mance da lamurra masu muhimmanci da suka faru yayin juyin juya halin Musuluncin na Iran irin su yunkurin 19 ga waan Dey na shekarar 1356 da kuma na ranar 9 ga watan Dey 1388 inda ya ce: Kiyayyar da ma’abota girman kai suke nuna wa al’ummar Iran, ba kiyayya ce mai karewa ba. A saboda haka wajibi ne jami’an gwamnati, ta hanyar dogaro da karfin da ake da shi na cikin gida, su yi kokari wajen raba makiya da makamin takunkumi da suke tinkaho da shi. Sannan su yi kokari wajen sauke nauyin da ke wuyansu na tabbatar da koyarwar wannan juyin.
Haka nan kuma yayin da yake taya al’umma murnar zagayowar ranar haihuwar Ma’aikin Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa) da jikansa Imam Sadiq (amincin Allah ya tabbata a gare shi), Ayatullah Khamenei ya bayyana yunkurin 19 ga watan Dey na shekarar 1356 a matsayin wani lamari mai cike da tarihi da kuma ayyana makoma. Daga nan sai ya ce: Akwai kokarin da wasu suke yi na sanya a mance da lamurra masu muhimmanci da suka faru cikin wannan juyin juya hali na Musulunci. To amma matukar al’umma suka kasance a raye sannan kuma aka ci gaba da samun mutane muminai masu son fadin gaskiya, lalle hakan ba za ta faru ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ci gaba da kiyaye ranaku masu muhimmanci da suka shafi juyin juya halin Musulunci irin su ranakun 19 ga watan Dey 1352, 22 ga watan Bahman 1357 (ranar da juyin juya halin Musulunci yayi nasara a Iran) da kuma 9 ga watan Dey 1388 (ranar da al’ummar Iran suka fito don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci sakamakon rikicin da ya barke bayan zaben shugaban kasa a shekara ta 2009) da sauransu a matsayin wani gagarumin kokari inda ya ce: Makiyan gwamnatin Musulunci ta Iran sun damfara fatansu kan matasan da suka biyo bayan nasarar juyin juya halin Musuluncin don su raba su da wannan juyi na Musulunci. To amma wadannan matasan su ne dai suka haifar da gagarumin yunkurin ranar 9 ga watan Dey da kuma turbude hancin mutanen da suke kokarin kautar da tafarkin wannan juyi ta hanyar haifar da fitina.
Har ila yau kuma yayin da yake sake jaddada muhimmancin da wannan yunkuri na al’ummar Qum yake da shi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Yunkurin 19 ga watan Dey mafari ne na wani gagarumin yunkuri na gama-gari a kasar nan. Sannan kuma al’ummar Iran suka shigo fagen fada da gwamnatin dagutu (Shah) inda daga karshe suka tumbuke gwamnatin zalunci ta ‘ya’yan gidan sarautar Shah.
Daga nan kuma sai Ayatullah Khamenei yayi ishara da wasu siffofi munana da gwamnatin ta Shah ta kebanta da su inda ya ce: Bakin zalunci da mulkin kama karya, amfani da mafi munin hanyar azabtarwa a gidajen yari, daya ne daga cikin siffofin gwamnatin ‘ya’yan gidan sarautar Pahlawi. Amma a wancan lokacin dukkanin masu ikirarin kare hakkokin bil’adama a yau sun kasance masu taimako da goyon bayan irin wancan gwamnatin.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da hannun da sahyoniyawa da Amurkawa suke da shi wajen samar da ‘yan sandan tsohuwar gwamnatin Shah (SAVAK) da kuma samar da yanayi na amfani da karfi da zalunci a cikin kasar Iran, Jagoran ya ce: Tona asiri na baya-bayan nan da aka yi dangane da irin azabtarwa da kuma gidajen yari na boye da kungiyar leken asirin Amurka CIA suke da su, lamari ne da ke nuni da rashin ingancin ikirarin da Amurkawa suke yi na goyon bayan fadin albarkacin baki.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana dogaro da manyan kasashen duniya cikin wulakanci a matsayin wata siffa da tsohuwar gwamnatin Shah ta Iran da kebanta da ita, daga nan sai ya ce: A wancan lokacin siyasar tsohuwar gwamnatin ta ginu ne bisa kare manufofin kasashen waje musamman Amurka bugu da kari kan wulakantawa da kaskantar da al’ummar Iran.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Babban dalilin kiyayya da gabar da Amurka take ci gaba da yi da al’ummar Iran da juyin juya halin Musulunci shi ne kasa mai girman matsayi da muhimmanci irin Iran ta kubuce musu sakamakon nasarar juyin juya halin Musulunci.
Siffa ta uku da Jagoran ya bayyana tsohuwar gwamnatin ta Shah da ita, ita ce faruwar nau’oi daban-daban na fasadi da lalata ta kudi da kyawawan halaye tsakanin manyan jami’an gwamnati. Daga nan sai ya ce: Babu wanda ya damu da batun lalacewar mutane kamar yadda kuma ra’ayi da mahangar mutane ba su da wata muhimmanci. Babu wata alaka tsakanin gwamnati da mutane.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana rashin damuwa da ci gaban ilimi, kwadaitar da rashin dogaro da kai, kambama al’adun kasashen yammaci, kwadaitar da mutane zuwa da kwadayin kayayyakin da ake shigowa da su daga waje maimakon na cikin gida bugu da kari kan lalata ayyukan noma da masana’antu na kasa a matsayin wasu daga cikin bakaken ayyukan tsohuwar gwamnatin ta Iran. Daga nan sai ya ce: Al’ummar Iran ma’abociyar hikima da sanin ya kamata, saboda ganin irin wannan wulakanci da kaskanci ne, ya sanya ta yunkurawa karkashin jagorancin wani babban bawan Allah, wato marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma samun nasara.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: irin nasarori da ci gaban da aka samu, haka nan kuma da farkawar da kuma irin matsayi mai girma da al’ummar Iran take da shi a yankin nan, an cimma dukkanin wadannan abubuwan ne sakamakon kawar da lalatacciyar gwamnatin zalunci da gidan sarautar Pahlawi.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da mafarin kiyayyar da ma’abota girman kai suke yi da al’ummar Iran bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Bai kamata wani ya yi tunanin cewa makiya za su kawo karshen irin wannan kiyayya da suke nunawa.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A lokacin da kuka gafala daga makircin makiya sannan kuka dogara da su, to kuwa makiyan za su yi amfani da wannan damar wajen cimma manufofinsu a kasar nan. To amma a lokacin da kuka tsaya kyam da kuma fahimtar hakikanin makiyan, to kuwa babu yadda ma’abota girman kan za su yi face janye wannan kiyayya ta su.
Jagoran ya bayyana matsin lambar da masu takama da karfi suke yi ga al’ummar Iran a halin yanzu da cewa hakan ya samo asali ne sakamakon kiyayyarsu maras karshe ga al’ummar ta Iran. Don haka sai ya ce: Duk da cewa akwai gagarumar tazara tsakaninmu da isa ga hakikanin koyawar wannan juyi irin su tabbatar da adalci tsakanin al’umma da kyawawan halaye na Musulunci, to amma sabanin maganganu marasa tushe da wasu suke fadi dangane da rashin nasarar al’ummar Iran, a halin yanzu al’ummar Iran ta samu gagarumar nasara da ci gaba a tafarkin da take kai.
Haka nan kuma yayin da yake sukan mutanen da suke rufe idanuwansu kan irin ci gaban ilimi da al’ummar Iran ta samu, Jagoran ya ce: Da wani dalilin kuke inkarin irin ci gaban ilimin da aka samu wadanda hatta cibiyoyin kasa da kasa sun tabbatar da hakan da kuma sanya shakku cikin irin nasarorin da aka samu wadanda hatta makiya sun tabbatar da hakan?
Ayatullah Khamenei ya yi ishara da abubuwan da suka faru a farko-farkon Musulunci inda ya ce: Lalle har yanzu ba a cimma dukkanin wadannan koyarwar ba, to amma abin da ke da muhimmanci shi ne ana ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki don cimma wadannan koyarwar. Kuma a yau al’ummar Iran suna ci gaba da riko da kuma bin wannan tafarkin da dukkan karfinsu.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi karin haske kan abubuwan da ya kamata a ba su muhimmanci a halin yanzu, inda ya bayyana hadin kai na kasa a matsayin daya daga cikin mafiya muhimmancin wadannan lamurra.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa rarraba kan al’umma, da kowane irin dalili ne kuwa, lamari ne da zai cutar da manufofin al’umma da kuma juyin juya halin Musulunci.
Haka nan kuma a wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana taimakon jami’an gwamnati wajen sauke nauyin da ke wuyansu a matsayin wani nauyi da ke wuyan kowa sannan kuma yayin da yake ishara da wajibcin dogaro da irin karfi na cikin gida da ake da shi, ya bayyana cewar: Su ma jami’an gwamnatin wajibi ne su san cewa abin da kawai zai kara musu karfin sauke nauyin da ke wuyansu shi ne dogaro da mutane da kuma irin karfi na cikin gida da ake da shi.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da takunkumin zalunci da aka kakabawa Iran, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Wadannan takunkumin sun haifar wa kasar nan da matsaloli, to amma idan har makiya suka sanya yin watsi da tushen wannan juyin ciki kuwa har da yin watsi da koyarwar Musulunci da kuma ‘yanci da ci gaban ilimi da ake samu a matsayin sharadin dauke wadannan takunkumin, to ko shakka babu, babu wani jami’in gwamnatin da zai amince da hakan.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Koda yake a halin yanzu a fili makiyan ba sa nuna damuwarsu kan wadannan koyarwar, to amma matukar aka ja da baya da kuma yin kasa a gwiwa, to kuwa za su da sannu a hankali za su koma kan wadannan koyarwar. A saboda haka wajibi ne a yi taka tsantsan, sannan kuma a fahimci maganganu da shawarwari da kuma ayyukan makiyan da kyau.
Jagoran ya bayyana samar da rigar kariya daga cutarwar wadannan takunkumi a matsayin hanya guda kawai ta takaita irin karfin makiya, daga nan sai ya ce: wannan ita ce asalin ma’anar tsarin tattalin arziki na dogaro da kai da aka gabatar. Tabbatar da hakan kuwa yana daga cikin manyan ayyukan jami’an gwamnati.
Haka nan kuma yayin da yake sake jaddada kiran da ya saba yi na kawo karshen dogaro da man fetur da ake yi, Jagoran ya ce: Bai kamata jami’an gwamnati su damfara fatansu ga ‘yan kasashen waje ba. Su san cewa komai kashin ja da baya da suka yi, to kuwa makiya za su kara matsowa. A saboda haka wajibi ne a yi tunani mai kyau, sannan kuma a yi amfani da karfi na cikin gida da ake da shi, ta yadda idan ma makiya ba su dage takunkumin da suka sa ba, to kuwa hakan ba zai iya cutar da ci gaban kasa da kuma walwalar al’umma ba.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wajibi ne a kwace makamin takunkumi daga hannun makiya. Don kuwa matukar dai kuka damfara fatanku ga makiya, to kuwa za su ci gaba da barin wadannan takunkumin. Kamar yadda a halin yanzu Amurkawa cikin dukkanin wauta suke fadin cewa matukar dai Iran ba ta sassauto kan wannan shiri na ta na nukiliya ba, to kuwa ba za a dauke dukkanin takunkumin da aka sanya mata ba.
Jagoran ya yi tambayar cewa: shin da hakan ne za a iya yarda da kuma amincewa da wannan makiyin?
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Ni dai ba na adawa da tattaunawa, to amma na yi amanna da cewa wajibi ne a damfara zukata ga wajajen da suke sanya fata na hakika, ba wai wajajen da babu tabbas a kansu ba.
A karshen jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Cikin yardar Allah jami’an gwamnati suna ci gaba da ayyukansu, don haka wajibi ne kowa ya taimaka musu. To amma su ma jami’an gwamnatin wajibi ne su yi taka tsantsan kada su dinga haifar da wasu lamurra da za su janyo kace-nace. Su yi kokari wajen kiyaye hadin kai da kuma amfani da irin himma da karfin gwiwan da al’umma suke da ita.
Ayatullah Khamenei ya bayyana makomar Iran da cewa makoma ce mai kyau daga nan sai ya ce: Da yardar Allah za a ci gaba da riko da tafarkin cimma manufofin wannan juyin. Sannan kuma da yardar Allah matasan wannan kasar za su shaidi wata ranar da za a tilasta wa azzaluman makiya rusunawa da mika kai.
2683018

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha