Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anadolu Agency cewa, a jiya dubban mutane sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a kasar Jamus domin nuna rashin amincewarsu da matakin da wasu ke dauka na nuna kiyayya ga musulmi a kasar saboda dalilai na siyasa.
Bayanin ya ci gaba da cewa a daidai lokacin da ake kai farmaki kan masallatai da cibiyoyin addinin musulunci da kan mata masu saka hijabi a Faransa da wasu kasashen turai bayan kai harin birnin Paris, fiye da mutane 35,000 sun gudanar da zanga-zanga a jiya a kasar Jamus domin nuna rashin amincewarsu da tsangwamar da ake nuna ma musulmi a cikin kasashen turai.
Kasar farnsa za ta karbi bakuncin manyan jami'an Gwamnatin kasashen turai. Kanfanin dillancin labarai na kasar faransa ya habarta cewa a gobe Lahadi shugaban kasar Faransa zai karbi bakuncin manyan jami'an Gwamnati na kasashen turai
Bayan zama a dan lokaci . a fadar milkin kasar faransa wato Palais lysee magaban za su halarci jerin gwano wanda aka shiya a birnin na Paris mai suna Marche Repubicaine domin nuna jumami da abinda ya faru ga kasar inda a cikin Makun nan aka kai hari kan gidan Mujallar nan ta barkonci mai suna tare da kashe ma'aikan Mujallar sha biyu.
Har ila yau ana sa ran Ministan harakokin kasar Rasha Sergy Lavrov tare da tawagarsa za su halarci wannan jerin gwano, rikicin wannan Maku na birnin Paris, kama daga harin Mujallar borkonci ta Charlie Hebro, garkuwa da Mutane a wani shago da wani kanfani yayi sanadiyar mutuwar Mutane sha bakwai.
2695327