IQNA

Adadin ‘Yan Sanda A New York Da Ke Karbar Musulunci A Masallacin Broklyan Na Karuwa

12:41 - January 12, 2015
Lambar Labari: 2699754
Bangaren kasa da kasa, Babban limamin masallacin Ayyub-Sultan da ke birnin New York na kasar Amurka ya sheda cewa, adadin 'yan sandan kasar Amurka da ke karbar addinin musulunci a wannan masallaci yana ci gaba da karuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Worl Bulletin cewaElyas Gonen  limamin masallacin Ayyub-Sultan da ke birnin New York na kasar Amurka ya sheda cewa, adadin 'yan sandan kasar Amurka da ke karbar addinin musulunci a wannan masallaci yana ci gaba da karuwa bayan fahimtar cewa addinin muslunci daban, ayyukan ta'addanci daban, babu abin da ya hada su.
Baytanin ya ci da cewa an jima ana takura ma mabiya addinin muslunci da ke gudanar da tarukan addini a wannan masallaci, ta hanyar aike musu da jami’an tsaron a farin da kuma ‘yan sanda  acikin kayan sarki da suna gudanar da bincike domin yaki da ayyukan ta’addanci, amma daga bisani sun fahimci cewa lamarin ba haka yake ba kamar yadda suka yi tsammani.
Yanzu haka dai wasu daga cikin jami’an tsaron da ake turawa zuwa wannan masallaci domin gudanar da ayyukan bincike suna karbar addini a lokacin da suke sauraren bayanan da ake yi ga mahakarta wurin, wanda kuma yana yin tasiri matuka a ciki kwakwalensu, inda limamin yak an karbi duk wanda ya bukaci shiga musulunci, tare da lakana masa Kalmar shahada.
Kasar Amurka na daga cikin kasashen da suke daukar matakai na takura mabiya addinin muslunci, bisa zargin ayyukan ta’addanci ba tare da wani dalili tabbabatace kan zargin ba.
2694142

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha