IQNA

Jaridar Charlie Hebdo Za Ta Sake Watsa Hotunan Zanen Batunci Ga Manzo (SAW)

15:33 - January 13, 2015
Lambar Labari: 2706237
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin lauyoyin jaridar Charlie Hebdo ta kasar ya bayyana cewa sakamakon harin da aka kai kan jaridar a gobe laraba za ta sake watsa wasu hotuna na cin zarafi ga manzon Allah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, Richard Maleka daya daga cikin lauyoyin jaridar Charlie Hebdo ta kasar ya bayyana cewa sakamakon harin da aka kai kan jaridar a gobe laraba za ta sake watsa wasu hotuna na cin zarafi da batunci ga manzon Allah (SAW) a matsayin wani mataki na daukar fansa.
Tun bayan harin da wasu matasa suka kai kan gidan jaridar ta Charlie Hebdo da ke birnin Paris na kasar Faransa a makon da ya gabata zuwa yanzu an kai hare-haren wuce gona da iri kan cibiyoyin Musulunci fiye da hamsin a kasar.
Cikin wata sanarwar da kungiyar musulmin kasar Faransa ta fitar a yau Litinin ta bayyana cewar tun daga lokacin da wasu matasa suka kai hari kan gidan jaridar Charlie Hebdo da ta yi zane-zanen batanci da cin zarafi ga Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w}, inda suka halaka ma’aikatan jaridar 12 a ranar Larabar makon da ya gabata zuwa yanzu an kai hare-haren wuce gona da iri kan cibiyoyin Musulunci a sassa daban daban na kasar fiye da hamasin kamar dai yadda bayani ya tabbatar.
Daya daga cikin masu magana da yawun kwamitin sanya ido a kungiyar musulmin Faransa ya bayyana cewar daga cikin hare-haren har da harbe-harben bindiga kan gine-ginen cibiyoyin Musulunci, baya ga aikewa da sakonnin barazanar kai hare-haren ta’addanci kan cibiyoyin na Musulunci a kasar.
2703993

Abubuwan Da Ya Shafa: Charlie
captcha