Bangaren kasa da kasa, shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Markel ta bayyana cewa addinin muslunci da musulmi wani bangare ne al’ummar kasar Jamus ya zama wajibi a tafi tare da su.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Cairo Portal cewa, Angela Markel shugabar gwamnatin kasar Jamus ta bayyana cewa addinin muslunci da musulmi wani bangare ne al’ummar kasar Jamus ya zama wajibi a tafi tare da su tare da nuna rashin amincewa da duk wani matakin tsangwama a kansu.
A daidai lokacin da ake kai farmaki kan masallatai da cibiyoyin addinin musulunci da kan mata masu saka hijabi a Faransa da wasu kasashen turai bayan kai harin birnin Paris, fiye da mutane 35,000 sun gudanar da zanga-zanga a jiya a kasar Jamus domin nuna rashin amincewarsu da tsangwamar da ake nuna ma musulmi a cikin kasashen turai musamman ma a kasar ta Jamus.
Wannan mataki da mahukuntan kasar ta Jamus suka dauka na nuna rashin amincewa da duk wani mataki na takura mabiya addinin muslunci ya harzuka masu tsatsauran ra’ayin kiyayya da musulmi, da ke neman a kori duk wani musulmi daga kasar, bisa hujjar cewa akasarin musulmin kasar baki ne, kuma addinin muslunci bakon addini ne akasar da ba za su amince da shi ba.
A cikin shekara ta 2010 Angela Mikel ta fadi irin wannan magana, tare da bayyana cewa a kowane lokaci mabiya addinin muslunbci suna iko da ‘yancin da su gudanar da harkokin addininsu a kasar Jamus kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya yarje musu da yin hakan.
Masu gaba da musulunci a kasar dai suna kallon wannan furuci tamkar dauke ma musulmi gindi ne, kuma hakan zai kara basu damar ci gaba da zama cikin ‘yanci maimakon hankoron da irin wannan kungiyoyi suke na takura ma musulmin domin su bar kasar.
2703944