Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na cibiyar kula da harkokin addinin muslunci da ke birtaniya, inda Malam Saeed Bahmapor zai gabatar da jawabi dangane da matsayin kur’ani da kuma bayanin ayoyinsa.
Wanann cibiya dai tana daukar nauyin shirya zama domin fadarwa a dukkanin ranakun Lahadi ga musulmi da ke zaune a birnin.
A lokacin gudanar da irin wannan zama dai Hojjatol-Islam Sheikh Ahamd Hanif ne kan gabatar da jawabai a bangarori daban-daban da suka shafi addinin muslunci, da kuma yadda ya kamata musulmi ya yi koyi da abin da addininsa ya shimfida masa.
2706236