IQNA

Wajabcin Yin Aiki Tare Tsakanin Kasashen Turai Da Na Musulmi Domin Yaki Da Ta’addanci

22:51 - January 21, 2015
Lambar Labari: 2742219
Bangaren kasa da kasa, kungiyar tarayyar turai ta bayyana butar da take da ita na ganin an kafa wani kwamiti tsakaninta da kasashen musulmi domin yaki da tsatsauran ra’ayi.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, a cikin wannan mako kungiyar tarayyar turai EU ta bayyana butar da take da ita ta fuskar yaki da ayyukan ta’addanci ta hanyar kafa wani kwamiti tsakaninta da kasashen musulmi domin yaki da tsatsauran ra’ayi na ta’addanci a cikin kasashensu.
Wannan mataki dai ya zo bayan ganin cewa yanzu haka masu tsananin kiyayya da addinin muslunci a kasar Faransa na ta kara tsananta harinsu da cin zarafin musulmin kasar a cikin kasa inda ya kai har sau dari da sha shida a cikin mako biyu da suka gabata.
Bayanin y ace a kasar musulmi na ci gaba da fuskantar nuna kyama daga masu tsattsauran ra’ayin kin jinin addinin Musulunci. Mujallar Lopvan ta mako-mako da ake bugawa a kasar ta Faransa ta ce a cikin wannan shekarar ta dubu biyu da sha biyar nuna kin jinin musulmi a cikin kasar.
Kasashen da ke cikin kungiyar tarayyar turai dai suna ganin cewa irin matakin da suka dauka na nuna kyama ga addoinin mulsunci babban kure ne, domin da dama daga cikin muslmi bas u amince da abin d ‘yan ta’adda suke yi da sunan musulunci ba.
2736608

Abubuwan Da Ya Shafa: EU
captcha