Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na leral.net cewa, a ranar Juma’a da ta gabata an gudanar da zanga-zangar kare martabar manzon Allah (SAW) a garin Zingishour da ke kudancin kasar Senegal tare da yin tir da Allah-wadai da jaridar Charlie Hebdo ta kasar Faransa kan zanen batuncin da ta yi.
Kwanaki biyu bayan fitowar jaridar nan ta faransa Charlie Hebdo data sake yin zanen batanci ga annabi Muhamed (SAW), musulmi da dama ne suka fito jiyya juma'a domin nuna bacin ran su gameda cin mutuncin da jaridar tayi ga addini islama.
Hakan dai ya kasance ta hanyar zanga-zanga a kasashen musulmai da dama jim kadan bayan kamala sallar juma'a. A wasu kasashen Afrika da suka hada da Senegal da sauransu an gudanarda zanga-zanga ta yin allawadai da wanan mujallar dama mahukuntan faransa da duk sauran shugabannin da suka halarci ganganmin goyan bayan jaridar a birnin Paris.
Idan dai a sauran kasahen nahiyar zanga-zanga ta gudana cikin lumana, a jamhuriya Nijar zanga-zanga tayi muni sosai inda mutane hudu suka rasa rayukan su yayinda wasu arba’in da biyar na daban suka jikata ciki kwa harda jami'an tsaro ashirin da biyu.
2757811