IQNA

17:01 - January 24, 2015
Lambar Labari: 2757916

Kin Jinin Musulmi Yana Karuwa A Faransa Fiye Da Kowane lokaci

Bangaren kasa da kasa, Charlie Hebdo tun bayan da batuncin da ta buga addinin muslunci a kasar Faransa musulmi na ci gaba da fuskantar nuna kama daga masu tsattsauran ra’ayin kin jinin addinin Musulunci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na MLP cewa, mujallar Lovan ta mako-mako da ake bugawa a kasar ta Faransa ta ce; A cikin wannan shekarar ta dubu biyu da biyar nuna kin jinin musulmi a cikin kasar ta Faransa ya rubanya har sau biyu idan aka kwatantashi da shekarar da ta gabata.
Wannan mujallar ta ce daga ranar 7 ga watan Janairu zuwa tara a gare shi da aka kai wa mujallar Charili Hebdo hari, cutar da musulmin da aka yi a cikin wannan kasa ya rubanya. Cibiyar da ta ke fada da nunawa musulmi kama a faransa a cikin watan janairu kadai ta iya kididdiga hare-hare da barazanar kisa da aka kai wa cibiyoyin musulmi da kuma su kansu musulmin har sau dari da sha shida.
Shugaban Cibiyar mai fada da nuna kin jinin Musulunci a Faransa Abdullah Zikry ya ce; buga jaridar sau miliya 7 abin mamaki ne, ya kara da cewa wWannan wani irin yanayi mai wuya da aka jefa musulmi a cikinsa, saboda haka ya yi kira ga gwmanatin kasar ta Faransa da ta dauki mataki da gaske domin fada da shi.
Da dama musulmin kasar Faransa dai sun yi Allah wadai da harin da aka kai wa jaridar Charlie Hebdo, sai dai duk da haka ba su tsira ba daga fuskantar barazana da kai wa cibiyoyoyinsu na taruka da ibada hare-hare na makonnin da suka gabata.
2757809

Abubuwan Da Ya Shafa: Charlie
captcha