Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jardar Indepent cewa, har yanzu dai ana ci gaba da kara samun kyamar mabiya addinin mulsunci a cikin sassa na kasar Birtaniya a cikin wadannan lokuta musamman a tsakanin dalban makarantu.
Kamar yadda wata cibiya mai sanya idanu kan kula da kananan yara ‘yan makaranta musulmi a kasar Birtaniya (Tel Mama) ta bayyana a cikin wani rahotonta, a halin yanzu yara musulmi da ke zuwa makaranta ana nuna musu banbanci matuka kasantuwar su musulmi, inda ake danganta su da ‘yan ta’adda.
Wasu bayanai dai sun ce a lokaci guda kuma ana samun karuar masu karbar musulunci a kasar fiye da kashi sittin wadannan mutane ne dai sun nuna cewa sun karbi muslunci ne sakamakon binciken da suke gudanarwa wanda haka ne yaba su damar daukar kudirin karbaer musulunci, sakamakon abin da suka gano a cikinsa na koyarwa ta hakika wadda mutum dan addam ke samun kamala da ita a cikin rayuwarsa mai ma’ana kamar yadda suka tabbatar.
Hakan yana zuwa ne duk kuwa da cewa ana ta maganar ayyukan bata gari da ke bata sunan mus;nci sakamakon abin da ak shirya na bata sunan addinin ta hanyar yin amfani da wasu gurbatattun musulmin kuma bata gari da kuma jahilai na addinin muslunci.
Ita dai kasar Birtaniya na daga cikin kasashen turai da ke da yawan musulmi wadanda suke samun karuwa ta fuskar adadi a kowace rana, haka nan kuma musulmi suna zuwa kasar domin karatu da kuma neman ayyukan yi.
2757842