Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a wannan ganawa da ta gudana tsakanin bangarortin biyu, Sheikh Muhammad Alamin ya bayyana godiyarsa da jin dadinsa dangane da irin gagarumar gudunmawar da wannan jami’a take bayarwa wajen yada ilimin addini da kuma wayar da kan musulmi.
Haka nan kuma dangane da abubuwan da suke faruwa a duniyar musulmi kuwa, bangarotin biyu sun jadda muhimamncin yin aiki tare da juna a dkkanin bangaroti na ilimi da za su hada kan musulmi domin tunkarar barazanar da musulunci ke fuskanta daga makiya, da kuma cin zarafin da ake yi wa manzon Allah (SAW) ta hanyar yin zanen batunci a kansa.
Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Sayyid Moradi ya yi nuna farin cikinsa matuka dangane da irin gagarumin ci gaban da ake samu tsakanin musulmi na wannan yanki, da kuma kara samun fahimtar juna da gane muslunci na hakika da ke kira zuwa ga zaman lafiya da hadin da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiyansa, da kuma kaucewa duk wata matsala ko rashin fahimta da ka iya kawo Baraka tsakanin mabiya addinin muslunci.
Daga karshe dukaknin bangarorin biyu sun yi kira zuwa ga samar da wata babbar gamaya ta dukaknin bangarori na muslmi domin tunkarar kalu bale da ke gaban al’ummar musulmi baki daya, da kuma kare martabar wannan addini da kuma manzon Allah (SAW) daga cin zarafin da ake yi masa a wanann duniya ta yau.
2772414