Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jam’iyyar Alwifaq cewa, mahukuntan Bahrain a yau ne suke gudanar da shari’ar jagoran jam’iyyar Alwifaq babbar jamiyyar adawa a kasar Sheikh Ali Salman a gaban kuliya tun bayan da suka kame shia kwanakin baya.
Wannan shari’a dai tana zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar kasar suke ci gaba da yin bore da kuma neman a saki Sheikh Salman wanda ake tsare da shi bisa dalilai na siyasa, duk kuwa da matakan da mahukuntan suke dauka na yin amfani da karfi domin murkushe masu zanga-zangar.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun kwatanta gidajen kason kasar Bahrain da gidajen kason gwamnatin 'yan nazy a kasar Jamus karkashin jagorancin shugaban kungiyar a wancan lokaci.
A cikin wani bayani da wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama suka fitar jiya daga wata babbar cibiyarsu da ke birnin London na kasar Birtaniya, sun bayyana irin matakan da mahukunatan kasar Bahrain suke dauke a cikin gidajen kaso wajen azabtar da 'yan adawar siyasa da cewa ya wuce haddi na 'yan adamtaka.
Bayanin ya kara da cewa masarautar Bahrain tana azabtar da 'yan adawar siyasa a gidajen kaso da hakan kan kai su ga rasa rayukansu ko wasu bangarorin jikinsu, inda ake yin amfani da duk wani salon a azabtarwa da a kan masu adawa da salon siyasar gidan sarautar kasar.
Kungiyoyin suka ce masarautar Bahrain ta hana kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa su ziyarci mutanen da ake tsare da su a kasar, tare da hana ganawa da mutanen da suka rasa danginsu sakamakon ukubar da masauratar ta Bahrain ta gana musu a gidajen kaso.
2772380