Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, yawan mutanen da suka rasa rayukan su bayan harin kunar bakin wake da aka kai a wani masalacin mabiya mazahabar shi'a dake kudancin kasar Pakistan ya kai akalla 60 da jikatar wasu goma na daban.
Harin dai na wanan juma'a ya auku ne a daidai locacinda al'umma garin Shikarpur dake nissan kilomita dari biyar daga birnin Karashi ke gudanarda sallah juma'a.
Da yake tabbatarda hakan ga masu aiko da rahotanni ministan lafiya na yankin Jam Mehtab Daher ya ce addadin wadanda suka riga mu gidan gaskia ya karu zuwa 60, kuma yanzu haka a ajiye gawawakin muatne hamsin da hudu a babbar asibitin lardin, kuma bakwai daga cikin su sun cika ne a assibitin.
Wanan dai shine wani hari mafi muni da aka fuskanta a wanan kasar tun bayan na watan Disamba bara wanda mayakan Taliban suka kai inda wata makarantar wanda yayi sanadin mutuwar yara dari da hamsin a lardin Peshawar dake arewa maso yammacin kasar.
2789264