IQNA

A Ranar 22 Ga Watan Bahman Al’ummar Kasa Zata Bai Wa Maras Da Kunya

21:08 - February 08, 2015
Lambar Labari: 2824836
Bangaren siyasa, A safiyar yau Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya gana da kwamandoji da jami'an rundunar sojin sama da dakarun kare sararin samaniyya na Iran, inda y ace ranar 22 ga watan bahman rana ce da makiya za su sha kunya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora na yanar gizo cewa, A jawabinsa yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da dalilai da manufar kiyayyar shekaru 36 da Amurka ta ke yi da al'ummar Iran da kuma kokarinta na dunkufar da kuma kaskantarsu, kamar yadda yayi nuni da hikimar da Iran take nunawa wajen tattaunawar da take yi da su kan shirin nukiliyanta da kuma kokarin Amurkan na tilasta wa Iran mika wuya inda ya ce: A ranar 22 ga watan Bahman al'ummar Iran za su nuna wa duniya cewa ba za su taba mika kai ga masu tinkaho da karfi ba, sannan kuma za su mayar musu da martani mai kaskantarwa a wannan ranar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wannan rana ta 19 ga watan Bahman 1375  ranar da dakarun sama na Iran suka yi mubaya'a ga marigayi Imam Khumaini (r.a) a matsayin wani lamari mai muhimmanci da ke dauke da darussa masu yawa a cikinsu inda ya ce: Irin jaruntakar da kwamandoji da jami'an sojin sama suka nuna a ranar 19 ga watan Bahman 1357, lamari ne da ke nuni da yadda maganar gaskiya da daukar hankula ta juyin juya halin Musulunci ta sami nasarar kutsawa cikin zukatan sojojin sama na gwamnatin Shah na wancan lokacin wadanda suka zamanto abin kauna da kuma fatan Amurka.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan wajibcin fahimta da kuma kiyaye wannan hakikar, Jagoran yayi ishara da wasu batutuwa masu muhimmanci da suka hada da irin tasirin da juyin juya halin Musulunci ya yi inda ya ce: Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma yadda al'ummomin duniya suka ga irin jaruntakar da al'ummar Iran suka nuna wajen tsayawa kyam a gaban girman kan Amurka, nan da nan suka zo da kuma riko da sakon juyin juya halin Musulunci.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A bangare guda kuma, ma'abota girman kai karkashin jagorancin Amurka, tun a ranar farko na nasarar juyin babu wata hanyar da ba su bi ba wajen dunkufar da wannan gagarumin yunkuri. Har zuwa yau din nan kuwa sun ci gaba da nuna wannan kiyayyar.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Kiyayyar Amurka da ma'abota girman kai ba wai ga daidaikun mutane ba ne, kiyayyarsu ga wannan yunkuri da matsaya wacce take tafiya tare da tsayin daka da neman ‘yanci da daukaka ta al'ummar Iran ne.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da maganganun wasu ‘yan siyasar Amurka cikin shekarun baya-bayan nan da ke nuni da irin gaba da kiyayyar da suke yi da al'ummar Iran, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Suna fushi ne da irin tsayin dakan al'ummar Iran, babbar manufar Amurka da kawayenta shi ne dunkufar da al'ummar Iran, wanda tabbas sun yi kuskuren lissafi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar irin wannan kuskuren lissafin ne ya sanya Amurka ci gaba da shan kashi cikin batutuwa daban-daban da suka shafi yankin Gabas ta tsakiya musamman kan abin da ya shafi Iran. Jagoran ya ce: Daya daga cikin misalan wannan kuskuren, shi ne maganar da wani jami'in Amurka yayi kwanakin baya inda ya ce Iraniyawa suna cikin tsaka mai wuya a tattaunawar da suke yi kan shirin nukiliyansu.
Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Lalle a ranar 22 ga watan Bahman, za ku ga yadda al'ummar Iran za su fito. A wannan ranar ce zai bayyana wa kowa shin al'ummar Iran suna cikin tsaka mai wuyan ne?
Jagoran ya ci gaba da cewa: Babu wani lokaci da hannayen al'umma da jami'an kasar Iran ya zamanto a daure, sannan kuma a aikace sun tabbatar da hakan. A nan gaba ma za su ci gaba da nuna hakan ta hanyar jaruntaka da nasarorin da suke samu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Amurka ce take cikin matsaloli da tsaka mai wuya a halin yanzu. Wannan kuwa wani lamari ne da abubuwan da ke faruwa a yankin nan da ma wajensa ke tabbatar da shi.
Yayin da yake ishara a shan kashin siyasar Amurka a Siriya da Iraki da Labanon da Palasatinu da Afghanistan da Pakistan, haka nan kuma ta kashin da take sha a kasar Ukraine, Ayatullah Khamenei ya kirayi Amurkawan da cewa: Ku din nan shekara da shekaru kenan kuke shan kashi. Amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan sai ci gaba take samu don kuwa babu yadda za a iya kwatanta da shekaru talatin din da suka gabata.
Haka nan yayin da yake ishara da irin ci gaba da Iran take samu a fagagen ilimi da fasaha, cikin lamurra daban-daban na zamantakewa, cikin lamurra na kasa da kasa bugu da kari kan irin tasirin da take da shi a yankin Gabas ta tsakiya da kuma irin matsayin da juyin juya halin Musulunci ya samu a cikin zukatan matasa, Jagoran cewa yayi: Jamhuriyar Musulunci ta Iran albarkacin irin wannan kwarewa da karfi da take da shi, tana ci gaba da samun ci gaba, alhalin Amurkawa sun gaza wajen kawo karshen wannan ci gaban, hakan ne ya tilasta musu yarda Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ko shakka babu makirce-makircensu a fagen siyasa, tsaro, tattalin arziki da al'adu ba su iya hana irin wannan ci gaban ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyan kasar Iran da kokarin makiya na nuna gazawar Iran a wannan bangaren, daga nan sai ya yi ishara da wasu batutuwa dangane da tattaunawar nukiliyan.
Lamari na farko da Ayatullah Khamenei ya yi ishara da shi, shi ne nasara cikin yarjejeniyar da za a cimma kan shirin nukiliyan na Iran inda ya ce: Ni dai ba na adawa da cimma yarjejeniya, to amma ba zan taba amincewa da ‘mummunar' yarjejeniya ba.
Haka nan yayin da yake ishara da abubuwan da Amurkawa suke ta fadi na cewa ‘rashin cimma yarjejeniya shi ya fi maimaikon cimma mummunar yarjejeniya', Jagoran cewa ya yi: Ni ma dai wannan shi ne abin da na yi amanna da shi. Na yi imanin cewa rashin cimma yarjejeniya shi ya fi maimakon cimma yarjejeniyar da za ta zamanto mai cutarwa ga manufofin al'ummarmu, wacce kuma za ta share fagen kaskantar da al'ummar Iran mai girma.
Batu na biyu da Jagoran yayi ishara da shi, shi ne irin kokari ba kama hannun yaro da jami'an gwamnati da kuma tawagar Iran a wajen tattaunawar nukiliyan suke yi wajen kwace makamin takunkumi daga hannun makiya inda ya ce: Idan har hakan ta faru sannan kuma aka kwace makamin takunkumi daga hannun makiya, to lalle hakan abu ne mai kyaun gaske. Amma idan ma hakan ba ta faru ba, to wajibi ne kowa ya san cewa akwai hanyoyi da dama a cikin gida na dakile wannan yaki na takunkumi.
Ayatollah Khamenei ya kara da cewa: Idan har muka yi kokari sannan muka yi amfani da karfin da muke da shi yadda ya dace, to ko da ba su sami damar kwace makamin takunkumi daga hannun makiya ba, to kuwa za mu iya kashe kaifinsa.
Batu na uku da Jagoran yayi ishara da shi, shi ne ayyukan da suka yi daidai da hankali na Iran a yayin tattaunawar da kuma rashin hankali da son nuna karfi da daya bangaren da ake tattaunawa da shi din yake yi.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da jawabin shugaban kasar Iran na baya-bayan nan da inda ya ke cewa ma'anar tattaunawa ita ce kai wa ga wani wajen da dukkanin bangarori biyu suka yi tarayyar kansa, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: A saboda haka ne bai kamata wani bangare yayi tunanin cewa abin da ya ke so ne wanda kuma ya saba wa hankali shi ne zai samu ba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Dabi'ar Amurka da wasu ‘yan kasashen Turai ‘yan amshin shatanta a yayin wannan tattaunawar, wata dabi'a ce da ta saba wa hankali. Abin da suke yi shi ne cimma dukkanin abin da suke so, alhali kuwa wannan ba ita ce hanyar tattaunawa ba.
Ayatullah Khamenei ya bayyana irin tsayin dakan da jami'an Iran suka yi a gaban irin wuce gona da irin bangaren da ake tattaunawa da shi din a matsayin wani lamari da ke bisa ingantacciyar turba. Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin siyasar da ta yi daidai da hankali na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a lokuta daban-daban ciki kuwa har da lokacin kallafaffen yaki da amincewa da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 598 (da ya dakatar da yakin) da kuma batutuwa daban-daban da suka biyo bayan kallafaffen yakin, Jagoran cewa ya yi: Dangane da wannan batu na nukiliya ma Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi amfani da hankali ne da aiwatar da abubuwan da suka daidai da hankalin, to amma abokan hamayyarmu kan babu wata hikima cikin halayensu, face dai abin da suka sa a gaba shi ne son amfani da karfi.
Jagoran ya kara da cewa: Ko da wasa al'ummar Iran ba za su taba mika wuya ga son amfani da karfi da tursasa da kuma duk wani abin da ya saba wa hankali ba.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ni na yarda da ci gaba da tattaunawa da kuma cimma yarjejeniya mai kyau, kuma ko shakka babu al'ummar Iran ma ba za su yi adawa da duk wata yarjejeniya da za ta kiyaye musu daukaka da kuma girmama su ba.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Wajibi ne a kiyaye girma, hurumi da kuma ci gaban al'ummar Iran a duk wata tattaunawa da za a yi. Don kuwa wannan al'ummar ba ta saba da amincewa da tursasawa da tinkaho da karfi na wani ba ciki kuwa har da Amurka da sauransu.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan batutuwan da aka gabatar a yayin tattaunawar dangane da cimma yarjejeniya mai matakai biyu, wato da farko dai a fara cimma yarjejeniya kan manyan lamurra kana daga baya kuma a je ga kananan batutuwa, Jagoran cewa yayi: Wannan yarjejeniyar dai ba abar yarda ba ce. Don kuwa kwarewar da muke da ita da kuma abubuwan da suka faru a baya suna nuni da cewa cimma yarjejeniyar kan manyan abubuwa suna share fagen da matsin lamba cikin kananan abubuwan.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Wajibi ne yarjejeniyar da za a cimma ta zamanto a mataki guda ne wacce kuma ta kumshi manya da kananan abubuwa tare.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Wajibi ne kuma abubuwan da yarjejeniyar ta kumsa su zamanto a fili da kuma rufe duk wata kafa ta tawili. Haka nan kuma bai kamata yarjejeniyar ta zamanto ta yadda daya bangaren, wanda da man ya saba mummunar amfani da damar da ya samu, ba zai samu damar mummunar amfani da damar ba.
Jagoran ya ce: Da yardar Allah, a ranar 22 ga watan Bahman al'ummar Iran za su nuna wa duniya cewa duk wani mutumin da yake son kaskantar da wannan al'umma, to kuwa zai fuskanci gagarumin bugu (daga wajen wannan al'ummar).
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Dukkanin al'ummar Iran da sauran al'ummomin da suke kaunarsu sun yi tarayyar sun yi amanna da cewa daukaka ta kasa ga wata al'umma wani lamari ne mai matukar muhimmanci. Don kuwa matukar aka rasa daukaka ta kasa, to kuwa ba za a taba samun tsaro da ci gaba ba. A saboda haka wajibi ne a kiyaye daukaka ta kasa. Wannan kuma wani lamari ne da jami'an gwamnati suka san da shi.
A karshe Ayatullah Khamenei ya ce: Da yardar Allah, al'ummar Iran ta hanyar fitowar da za su yi ranar 22 ga watan Bahman, za su dunkufar da makiyansu har kasa.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai, sai da babban hafsan hafsoshin sojin sama na Iran Air Mashal Hasan Shahsafi ya gabatar da jawabi da kuma gabatar da rahoto kan irin ayyukan da rundunar sojin sama na Iran suka yi da kuma irin nasarorin da suka samu ciki kuwa har da kera jiragen saman yaki na zamani.
2822537

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha