IQNA

Musulmin Kasar Malawi Na Yada Sakon Addinin Muslunci

19:42 - February 09, 2015
Lambar Labari: 2829311
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Malawi sun fara gudaar da ayyuka na isar da sakon muslunci karkashin kungiyar IIB zuwa kasashen ketare da ke makwaftaka da kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, Dinala Chabolika daya daga cikin shugabannin mabiya addinin muslunci a kasar ta Malawi ya bayyana cewa, za su ci gaba da ayyukan da suka fara na yada addinin muslunci zuwa al'ummomin kasashen da suke da makwaftak ada kasar.

Kasashen Zambia da Zimbabwe kasashe ne na kiristoci zalla wadanda suke bin addinin masihiyanci, wadanda musulmin kasashen ba su  wuce kashi 2 cikin dari ban a mutane miliyon 15 a Zimbabwe, sai kuma kashi 1 cikin mutane miliyan 13 a Zambia.

Kungiyoyin musulmi na kasar sun nuna gamsuwarsu matuka da irin namijin kokarin da wannan cibiya take na yada addinin muslunci da kuma wayar da kan mutane zuwa ga fahimtar hakikanin sakon addini na gaskiya, tare da nuna musu abin da ake dora su a kansa na cewa muslunci ta'addanci ne ba gaskiya ba ne.

An kafa wanann bababr cibiyar musluncia  a kasar Malawi ne a cikin shekara ta 1990 wadda kuma har yanzu take ci gagbab da gudanar da aikinta na wayar da kan jama'a musulmi da wadanda ba musulmi ba, inda take koyar da musulmi ayyyuka na ibda da tarbiya, yayin da kuma wadanda ba musulmi a take nuna musu koyarwar musulunci.

A halin yanzu dai akwai musulmi da adadinsu ya kai kashi 36 cikin dari na dukkanin muatne kasar Malawi da suka kai miliya 16, kuma wannan adadi yana ci gaba da karuwa.

2829231

Abubuwan Da Ya Shafa: malawi
captcha