Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a yau ce miliyoyin mutanen kasar Iran suka gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya ga juyin juya halin Musulunci a kasar shekaru 36 da suka gabata.
Kafofin yada labarai na kasar Iran sun bayyana cewa manya manyan jami’an gwamnati da sojojin kasar da kuma sauran mutanen gari ne suka halarci tattakin cika shekaru 36 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran.
Bayanin ya kara da cewa an sami manya manyan baki kimani dari hudu daga kasashen waje wadanda suka halarci tattalin, an kuma daga tutoci da ke cewa (Labbaika Ya Rasulullah) sannan kafafen yada labarai da dama na ciki da waje ne suka halarci bukukuwan.
A nan tehran dai miliyoyin mutane ne suka taro a dandalin yanci da ke tsakiyar birnin inda aka kammala tattakin da.
Taken jerin gwanon na bana dais hi ne nuna goyon baya ga manzon Allah Muhammad (SAW) a dukkanin fadin kasar baki daya, kauyuka da birane.
2835878