Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar Press TV cewa, an janazar mutanen Shaddy Barakat 23, da matarsa Yusor Mohammad Abu-Salha 21, da kuma 'yar uwarta Razan Mohammad Abu-Salha 19 a yankin nasu.
Wannan ya zo ne a daidai lokacin da kasashen yammacin turai da kafofin yada labaransu suka dukufa wajen magana kan batun ta'addanci da kuma wajabcin daukar dukkanin hanyoyin shiga kafar wando daya da 'yan ta'adda.
Jim kadan bayan faruwar lamarin labarin ya watsu a ko'ina cikin fadin duniya ta hanyoyin sadarwa daban-daban da suka hada da hanyoyin sadarwa na yanar gizo, inda labarin ya harzuka miliyoyin musulmi a duniya, da ma sauran mutane masu lamiri na 'yan adamtaka, inda dubban musulmi yanzu haka suke ci gaba da fitowa akasashe daban-daban suna nuna rashin amincewarsu da hakan, tare da neman mahukuntan Amurka da su dauki matakin yin adalci kan wannan lamari.
Duk da cewa jami'an tsaron kasar ta Amurka sun kame mutumin da ya ikata wanann danyen aiki, to amma shakku shi ne irin shari'ar da za a yi masa shin ko za ta kasance ta adalci, wadda za ta yi hukunci daidai da abin da ya aikata.
Wani abu kuma wanda shi ne ya fi ban mamaki dangane da wannan lamari shi ne, yadda gwamnatocin kasashen yammacin duiya da kafofin yada labaransu suka yi gum da bakunansu kan wannan ta'asa da aka aikata kan muslmi, musamamn ma ganin cewa ba da jimawa ba ne aka kai hari kan ofishin jaridar Charlie Hebdo ta kasar Faransa da ke cin zarafin addinin muslunci, inda duk duniya ta ca a kan batun, tare da nuna goyon bayan ga jaridar, har ma da halartar wasu shugabannin kasashen duniya a kasar faransa domin taya wanann jarida alhini kan kashe ma'aikatanta da kuma yin Allawadai da ta'addanci, amma kuma ba a ji duriyar shugabannin da suka taru a Faransa da kafofin yada labarai na duniya kan kisan ta'addancin da aka yi kan musulmin Amurka ba, wanda hakan ke nuni da harshen damo a cikin yadda ake kallon ta'addanci da ake dangata shi da musulmi da kuma ta'addancin da wasu ke aikatawa kan musulmi, abin jira dai a gani a halin yanzu shi ne matakin da ita gwamnatin Amurka za ta dauka kan wannan batu.