IQNA

Fushin Mutanen Tunis Kan shiru Na Kafofin Yada Labaran Turai Kan Kisan Musulmin Amurka

20:31 - February 16, 2015
Lambar Labari: 2858522
Bangaren kasa da kasa, daruruwan mutane sun gunar da gangami a kasar Tunisia domin nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda kasashen yammacin turai suka yi gum da bakunansu kan kisan musulmin Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, a jiya mutane da dama sun gunar da gangami a kasar Tunisia domin nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda kasashen yammacin turai da kafofin yada labaransu suka yi shiru kan kisan gilla da aka yi wa musulmi dalibai a kasar Amurka a cikin wannan mako.

Dangane da wannan batu mutum yana iya fahinta a fili, yadda kafafen yada labarai na yamma suka bambanta tsakanin kissan daliban jami’a musulmi da aka yi a wannan jami’a Jami’ar da kuma wanda aka yi ma’aikatan jaridar mako mako mai cin zarafin muslunci.

Haka zalika banda haka a lokacin da suka fara bada labarin ma sai, suka gurbata shi da cewa ai an kashe daliban ne a rikici tsakaninsu da makobcinsu kan wurin ajiye motoci a masaukin daliban Sun yi kokarin nunawa duniya cewa kisan bai da nasaba da addini wanda ya kashe ko wadanda aka kashe .

Ga misali tashar talabijin ta Amurka ta bada labarin kamar haka  wani mutumi ne ake tuhuma da kashe musulman ammam wannan tashar ta yada duk jawabin da shugaban kasar Amurka ya yi dangane da kisan majallar  Sannan ta kira wadanda suka kashe musulmi a matsayin wanda ake tuhuma, amma kai tsaye ta kira wadanda suka yi kisan paris a matsayin yan ta’adda.

Banda haka wasu sanannun mutane suka yi kira ga musulmi su nemi uzuri kan ayyukan ta’addanci na paris amma babu irin haka a lokacinda abin ya faru ya faru a Amurka a wannan karo.

Wannan halin haka yake a wurare da dama, inda shugaban kasar Amurka bai yi wata magana a kan wannan kisan ba sai bayan da musulmi suka yi zanga zanga har zuwa fadarsa.

2856228

Abubuwan Da Ya Shafa: tunisia
captcha