Kmafanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, Abdulazi Bin Usman Al-tuwaijari shugaban kungiyar ya bayyana cewa irin tsatsauran ra'ayi da ake samu yana da alaka da rashin fahimtar addinin muslunci, wanda a kowane lokaci yake kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninsa da sauran addinai.
Shi ma a nasa bangaren wanda ya jagoranci sallar juma'a a fadar mulkin jamhuriyar musunci ya bayyana cewa kungiyar 'yan ta'addan daesh da cewa tana aiwatar da manufofin yahudawa ne.
Shehin malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar hudubar sallar juma'a inda ya ce irin furucin da manyan malaman yahudawan sahyuniya ke yi a na cewa is wata baiwa ce daga Allah domin ta kare yahudawan sahyuniya hakan na tabbatar da cewa suna kan manufa guda, wadda ita ce bata sunan addinin muslunci a idon duniya, da ma rusa idan har za su iya samun damar yin hakan.
A cikin yan lokutan nan dai yayan kungiyar suna ci gaba da kaddamar da hare-harensu na ta'addanci a cikin kasashen musulmi, inda suke kashe tare da yin yankan rago a kan fararen hula musulmi, da kuma kone su, duk da sunan jihadi a tafarkin ubangiji.
2882590