Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-manar cewa, Sheikh Afif Nablusi babban malami daga cikin malaman shi'a a Lebanon ya bayyana ayyuakn ta'addanci da ake aikatawa da sunan muslunci da cewa babban hadari ga shi kansa muslunci da kuma sauran mutanen duniya.
Shehin malamin ya ci gaba da cewa bayyana ayyukan ta'addanci a cikin wannan zamani yana da alaka da irin mummunar akidar da aka samar ne tun wasu karnoni da suka gabata, wadanda suke da alaka da fatawoyin kafirta musulmi tare da halastar da jininsu saboda banbancin fahimta kawai.
Sheikh Afif nablusi ya ci gaba da cewa nauyi day a rataya kan malaman addinin muslunci da su mike wajen wayar da kan sauran mabiyansu da am al'umma baki daya, domin kwance kullin da aka kulla a cikin wanann mummuna akida ta kafirta musulmi, wadda kuma sakamakon abin da take dauke das hi ne ake ganin bayyana irin wadannan munan ayyka na ta'addanci da sunan musluncia duniya.
Daga cikin ayyukan da yayan kungiyoyin yan ta'adda suke aikata suna fakewa ko dogara da irin fatawowin da suka samu a cikin littafan malaman da suka gabata da ke dauke da akidar kafirta musulmi tun karnonin da suka gabata, daga ciki kuwa hard a fatawowin malamin da ake kira shehin muslunci.